1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tarihin Muhammadu Buhari

July 23, 2010

A yanzu dai Muhammadu Buhari ya koma jam'iyar CPC domin tunkarar zaɓe mai zuwa.

https://p.dw.com/p/OSLr
Muhammadu Buhari na jam'iyar CPC a NajeriyaHoto: AP

An haifi Janar Muhammadu Buhari ne a ranar 17 ga watan Disemba na 1942 a garin Daura a jihar Katsina. Buhari ya halarci makarantar Elementary ta Daura kafin ya koma mai'aduwa a jihar katsina. Ya halarci kwalejin katsina a shekarar 1953. Bayan kammala kwaleji ya shiga makarantar horas da sojoji dake Kaduna.

Janar Muhammadu Buhari ya zama ƙaramin hafsan sojin ƙasa tare kuma da halartar makarantun horas da sojoji a ciki da wajen Najeriya kama daga Indiya zuwa Amirka. Haka kuma ya riƙe muƙamai na soji da dama da suka haɗa da kwamandan dakarun sojin sulke dake Jos. Buhari ya zama Gwamnan jihar Arewa maso gabashin Najeriya da ta ƙunshi jihohin Adamawa da Taraba da Gombe da Bauchi da Yobe da kuma Borno na yanzu.

Bayan haka kuma ya zama ministan ma'aikatan man fetur da kuma shugaban hukumar matatan man fetur ta ƙasa NNPC na farko a shekarar 1977. Kafin ya zama shugaban Mulkin Sojan Najeriya daga ranar 31 ga watan Decemba,1983 zuwa 27 ga Augusta 1985, sakamakon juyin mulki da sojoji su ka yi wa gwamnatin farar hula ta wancan lokaci.

A ranar 27 ga watan Augustan shekarar 1985, Janar Ibrahim Babangida ya jagoranci kifar da gwamnatinsa. Buhari ya zama shugaban Hukumar kula da rarar man fetur  (PTF) da marigayi shugaban Najeriya Janar Sani Abacha ya kafa domin gudanar da aiyukan raya ƙasa da rarar kuɗin man fetur da akayi ƙari a lokacin.

A shekarun 2003 da kuma 2006, Janar Muhammadu Buhari ya tsaya takarar neman shugabancin Najeriya a jam'iyar ANPP, wanda Hukumar zaɓen ƙasar ta bayyana Jam'iyar PDP dake mulki a matsayin wadda 'yan takaranta suka samu nasara, a zaɓen da ƙungiyoyin da suka saka ido a zaɓen na ƙasa da ƙasa su ka ce cike yake da kura-kurai.

A yanzu dai Muhammadu Buhari ya fice daga cikin jam'iyar ANPP mai  adawa tare kuma da kafa  jam'iyar CPC domin tunkarar zaɓe mai zuwa.

Mawallafi: Babangida Jibril

Edita: Yahouza Sadissou Madobi