1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tarihin Lamidon Adamawa Barkinɗo Aliyu Mustapha

April 15, 2010

An haifi sabon Lamiɗon Adamawa Alhaji Muhammadu Barkinɗo Aliyu Mustafa a ranar 14 ga watan Fabrairun shekarar 1944 a garin Yola dake jihar Adamawa ta yanzu.

https://p.dw.com/p/Mx9I
Taswirar Nigeria dake nuna birnin Abuja a tsakiyaHoto: AP Graphics

An dai haifi sabon Lamiɗon na Adamawa Alhaji Muhammadu Barkinɗo Aliyu Mustafa a ranar 14 ga watan Fabrairun shekarar 1944 a garin Yola dake jihar  Adamawa ta yanzu. Kuma ya fara karatun sa na Firamare ne a Mubi  daga shekakar 1951 zuwa 1954. Bayan nan kuma ya halarci makarantar middle ta Yola a shekakar 1955.

Bayan da ya kammala makarantar middle a shekarar 1957 kuma ya halarci makarantar Firamare ta kwana dake Dutsen-Ma daga shekarar 1958 zuwa 59. kafin ya halarci sakandaren Zariya a shekakar 1960.

A shekarar 1965 ya halarci kwalejin Barewa dake Zariya daga nan ne kuma ya halarci Jami'ar Ahmadu Bello dake Zariyan, inda kuma ya samun shedar Diploma a harkokin shari'a daga shekarar 1967 zuwa 1969.

Tsakanin shekarun 1979 zuwa 1983 sabon lamiɗon ya zama kwamishinan aiyuka da lafiyan dabbobi na shekaru huɗu. Daga shekarar 1991 zuwa 2003 kuma Maimartaba Lamido yayi aiki da hukumar matatan manfetur ta ƙasa, ya kuma zama shugaban kamfanin gine-ginen hanyoyi ta Sterling dake kaduna. Kafin daga bisani ya zama shugaban hukumar gidan Radiyon Tarayya ta FRCN.

A shekarar 1980 ne dai marigayin Lamiɗon Adamawa Dr Aliyu Mustafa ya naɗa shi Ciroman Adamawa kuma wakili a Majalisar zartarwar Sarki.

Lamiɗon wanda keda takardar shedar Digirgir ta Dr ya halarci Jami'ar Saint Clement University dake West Indies a Birtaniya da kuma wasu kwasakwasan a nan Jamus inda ya ƙware a harkokin sufurin Jiragen ruwa. Haka kuma yayi aiki a matsayin jami'in kwastan.

Mawallafi: Babangida Jibril

Edita: Yahouza Sadissou