Tarihin Kurkukun Gontanamo | Amsoshin takardunku | DW | 13.09.2005
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Amsoshin takardunku

Tarihin Kurkukun Gontanamo

Takaitaccen tarihin Kurkukun Gontanamo da ke Kasar Kyuba

kurkukun gwantanamo

kurkukun gwantanamo

Masu sauraron mu assalamu alaikum barkan mu da sake saduwa cikin wani sabon shirin na amsoshin takardun ku,shirin dake amsa tambayoyin masu sauraro.

Tambaya: Fatawarmu ta farko a wannan makon ta hadin gwiwa ce, daga shugaba Dandilimi Jibo da uwar gidansa Malama Rakiya, Magama Gumau , akwatin gidan waya 756 Bukuru , Jos ta kudu, Jihar Filaton Tarayyar Najeriya. Suka ce don Allah muna so ku bamu tarihin Gidan kurkukun Gotanamo?

Amsa: Gontanamo dai wani sansani ne na sojojin Amurka da yake a Kasar Kyuba, kuma shikadai ne sansanin sojojin Amurka a wata Kasa Mai bin tsarin kwaminisanci. Shidai wannan sansani yana kudu maso yammacin Kasar ta Kyuba, kusan tafiyar mil 400 daga garin Miyami, kuma sama da mutanen Kasar Amurka kimanin 3000 ne a wannan sansani, wadanda suka hada da sojoji da farar hula da kuma iyalansu.

Wannan sansani ya samo asali ne daga tarihin tsohon tsarin sansanonin Amurka a Kasashen Duniya.Tsarawa da kuma sanya wannan sansani a kasar Kyuba ya faru ne tun lokacin da akai yaki tsakanin Kasar Amurka da Kasar Spain, lokacin da sojojin Amurka suka samu galaba akan sojojin Spain na rundunar “Caribbean’’ a kusa da garin Santiago da ke kasar Kyuba a shekarar 1898.

A shekarar 1903 ne dai Kasar Amurka ta karbi hayar yankin daga kasar Kyuba domin amfani da shi a matsayin tashar shan mai ga rundunau sojojinta na ruwa, amma a shekarar 1934 wa’adin yarjejeniyar da Kasashen biyu suka yi ya cika.

A lokacin da shugaban Kasar Amurka Eisenhower ya yanke huldar jakadanci da Kasar Kyuba a shekarar 1961 sai dubban ’yan gudun hijira na kasar Kyuba suka cika sansanin. Kai da shekara ta zagayo ma sai jamian sojan kasar ta Kyuba sukai kaura zuwa sansanin na watanni da dama, a lokacin rikici akan makamai masu linzami na kasar ta kyuba.

A shekara ta 1964 sansanin sojojin ruwan akan dole ya zama mai dogaro da kansa bayan shugaba Fidel Castro ya yanke wa sansanin wutar lantarki da kuma ruwansha.

A shekarar 1991 sansanin ya zama wani masauki na wucin gadi ga dubban masu kaura daga Kasar Haiti,wadanda suka gudu domin tsoron juyin mulkin sojoji a Kasar. Haka zalika a shekarar 1994 an yi wa wasu makauratan kimanin su 45,000 daga Cuba da Haiti masauki na wucingadi a wannan sansani.

Kamar yadda bayanai suka nunar daga kasar ta Amurka,babban burin wannan sansani shine, ya kasance a matsayin wani sansani na samar da kayayyakin aiki ga rundunar sojojin ruwa na yakin Caribbean.Jiddadan walahairan suna sintiri a kewayen sansanin.

To tunidai sansanin na Guantanamo Bay ya dawo cikin Labarun yau kullum,kuma a farkon shekara ta 2002 ne aka gina wani kurkuku a sansanin da ya haifar da kace-nace a halin yanzu,wanda a ke kira da Turanci (Camp X-Ray) in da ake tsare da musulmi ’yan gwagwarmaya musamman ma wadanda ake zarginsu da alaka da kungiyar Al-Ka’ida da Taliban.

 • Kwanan wata 13.09.2005
 • Mawallafi Abba Bashir
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BwXP
 • Kwanan wata 13.09.2005
 • Mawallafi Abba Bashir
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BwXP