1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tarihin Karishma Kapoor

Abba BashirDecember 4, 2006

Bayani akan Karishma Kapoor

https://p.dw.com/p/BvV7
Karishma a fim din Samara
Karishma a fim din SamaraHoto: AP

Jama’a masu sauraronmu assalamu alaikum, barkammu da wannan lokaci, barkammu kuma da sake saduwa da ku a cikin wani sabon shirin na amsoshin takardunku,shirin da yake amsa tambayoyin da ku masu sauraro kukan aikomana.

Tambaya:Fatawarmu ta wannan makon ta fito daga hannun Malama Fa’za Sallisou, Maradi, Niger. Malamar ta ce, Don Allah ina so ku ba ni tarihin hsahararriyar yar indiyannan, mai suna karishma kapoor.

Amsa: Karishma Kapoor da ake kira da suna Lolo an haife ta ne a ranar 25 ga watan yuni na 1974 a birnin Mumbai na kasar Indiya.mahaifinta Randhir Kapoor, shima wani shahararren dan-fim na India ne, a shekarun 1970 zuwa 1980, haka itama mahaifiyar ta yar-fim ce mai suna Babita. Karishma ta yi karatunta ne a makaranatar Cathedrala and John Canoon na Mumbai har zuwa sakandare.fim din daya fara fito da ita shine Prem Qaidi a 1991 tun daga nan ne kuma ta fara suna a cikin fim din India.

Bayan tayi aure, ta dan dakatar da fina-finan da take yi, amma ta sake komawa fim inda ta fara da fim mai suna Mee jeevan sathi cikin wannan shekara.Ta karbi lambobin yabo da dama na fina-finai da suka hada da Raja Hindustani da Zubeida da Fiza da dai sauransu.

Karishma kapoor tayi aure a ranar 29 ga watan satumba 2003,inda ta auri wani babban dan kasuwa Sunjay Kapur,bisa dokokin addinin Sikh.

Suna da ya guda mai suna Samaira,wacce aka haifa ranar 11 ga watan Maris na 2005. Ya zuwa yanzu dai, ta yi manyan fina-finai fiye da 60.