Tarihin Jean Bedel Bokassa | Amsoshin takardunku | DW | 04.03.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Amsoshin takardunku

Tarihin Jean Bedel Bokassa

Tarihin tsofan shugaban ƙasar Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya mirganyi Jean Bedel Bokassa

default

Jean Bedel Bokassa tsofan shugaban ƙasar Afirka ta Tsakiya

A yaushe ne shugaba Jean Bedel Bokassa yayi mulkin ƙasar Afrika ta tsakiya ? ta ƙaƙa ya zo mulki kuma ƙaƙa ya sauka daga kujera mulkin ? Tarihin Jean Bedel Bokassa na da matuƙar tsawo saidai a taƙaice an haife shi ranar 22 ga watan Febuaru nan shekara ta 1921 a wani ƙauye mai suna Bobangui.Kuma asulin iyayensa ´yan cirani ne, da suka zo daga ƙasar Cote d´Ivoire.Tun yana ɗan shekaru shida ya zama maraye, bayan da turawan mulkin mallakar ƙasar Faransa suka bindige ma´aifinsa. im kaɗan bayan haka itama ma´aifiyarsa ta kashe kanta. To amma kasancewar sa maraya ba uwa ba uba, ta ƙaƙa yayi karatu ya shiga siyasa har ya kai ga matsayin shugaban ƙasa ? Hausawa kan cewa wai ƙaddara ta riga fata. To bayan rasuwar iyayensa sai dangi sa suka karɓe shi suka tatala.Kuma sai ya kasance a makaranta yaro mai ƙwazo da basira, saboda haka ma sai maluman sa a lokacin turawan mulkin mallaka suka bukaci ya zama wani limamin krista, to amma sai ya fi nuna shawar shiga aikin soja.Ta haka ne ya shiga rundunar sojojin ƙasar Faransa a shekara 1939.Yayi yakin Indochine da Algeriya. A game da batun siyasa kuwa  ya shigi gadan gadan a shekara 1064 bayan da ɗan uwansa, shugaban ƙasar Afrika ta tsakiya na farko cewa da David Dacko ya naɗa shi shugaban rundunar sojoji ta ƙasa. Bayan an yi shekara guda sai wani daga cikin manyan sojojin ƙasar yayi yinƙurin  hamɓar shugaban ƙasa, ya kuma buƙaci cafke Bokassa, to saidai Allah bai bashi sa´a ba.Jean Bedel Bokassa yayi nasara murƙushe wannan yinƙurin juyin mulki, to amma a wani mataki na kogo ya juye da mujiya, sai yayi amfani da wannan dama, domin kifar da shugaban ƙasa David Dacko, to kaji yadda Bokassa ya hau karagar mulki a Afrika ta Tsakiya ranar 31 ga watan Disemba na shekara ta 1965. To bayan ya hau mulki ƙaƙa ya gudanar da harakokin jagorancin ƙasar ? Jim kadan bayan hawansa karagar mulki ya kawo cenje -cenje da dama, wanda kuma jama´a suka yi marhabin da su, mussamman ta ɓangaren noma da mallakar filayen noma da kuma yaki da cin hanci da rashawa.Duk da kama karya da ya shimfiɗa, yayi matuƙar farin jini ga jama´a a shekaru bakwai na farko, kuma mulkin nasa ya samu babban goyan baya daga ƙasar Faransa. To saidai tarmamuwar Bokassa ta fara dushewa tunranar biyu ga watan Maris na shekara ta 1975 inda ya aiyanar da kansa amatsayin shugaban ƙasa har sai ƙarshen rayuwarsa.Shekaru biyu bayan haka ya naɗa kansa Marshal. Sannan ya naɗa kansa sarkin sarakuna a watan Disemba na shekara ta 1977. Shin da gaske ne Jean Bedel Bokassa ya musulunta ? Ƙwarai kuwa wannan magana gaskiya ce.Jean Bedel Bokassa ya musulunta a shekara 1976 inda ya cenza suna zuwa Salah Eddine Ahmed Bokassa.A cewar rahotanin daga ƙasar, shugaban ƙasar Libiya ne Muhamar Ƙaddafi ya musuluntar da shi. Ta la´akari da kyakkawar karɓuwar da ya samu daga jama´a amma ta ƙaƙa kuma mulkin ya kufce masa ? Sanadiyar baƙin jinin Jean Bedel Bokassa ta samo asuli daga cenje cenje barkatai da yayi ta aikatawa da kuma mulkin kama karya da ya ƙaddamar.Misali a shekara 1979 ya umurci jami´an tsaro su fattataki ´yan  makaranta a lokacin wata zanga zanga, sannan an zarge da da hannu acikin kissan wasu ɗallibai 100 bayansu shirya zanga zangar nuna adawa da sanya kaya iri ɗaya a cikin makaranta.Sai kuma tuhumar sa da ake yi da leffin maita. A cikin wannan yanayi ne na taɓarɓarewar al´amura cikin a daren 120 ga watan Satumber na shekara ta 1979 a yayin da Bokassa ke ƙasar Libiya, jami´an leƙen asiri tare da hadin gwiwar ƙasar Faransa suka kadamar da wani hari da suka yi masa juyin mulki.Kuma shugaban ƙasar da ya hamɓare wato David Dacko shine ya sha fansa,kuma ya koma kan kujerarsa. Shikuwa Jean Bedel Bokassa ya shiga gudun hijira ƙasar Cote d´Ivoire sannan ya tafi Faransa.Ya koma Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya a shekara  1986 duk da cewar kotu ta yanke masa hukuncin kisa.Shigar sa ke da wuya kotu ta sa aka cafke shi an ka sake yi masa shari´a aka sake jaddada hukuncin kissan.Saidai kuma shekara ɗaya gabani, kotu ta sassauto hukuncin zuwa ɗaurin rai da rai, sannan ya koma ɗaurin shekaru goma.Shugaban ƙasa Andre Kolingba yayi masa afuwa gaba ɗaya  a shekara 1993. Jean Bedel Bokassa ya mutu sanadiyar ciwon bugun zuciya a shekara 1996. Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi Edita: Abdulahi Tanko Bala