1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tarihin Idi Amin Dada

Abba BashirOctober 24, 2005

Takaitaccen Tarihin Idi Amin Dada

https://p.dw.com/p/BvVl
Idi Amin Uganda
Idi Amin UgandaHoto: AP

masu sauraronmu asalamu alaikum barkan mu da sake saduwa daku a cikin wani sabon shirin na amsoshin takardunku,shirin dake amsa tambayoyin masu sauraro.

Tambaya-fatawarmu ta wannan makon ta fito ne daga hannun mai sauraron mu a yau da kullum,Hamisu Isah Sheka makaranta gidan mai kantu,dake cikin karamar hukumar Kumbotso ta jihar Kano a tarayar Nigeria,mai sauraron namu cewa yayi don Allah ku bani tarihin marigayin tsohon shugaban kasar Uganda Idi Aminu Dada.

Amsa-An haifi marigayi tsohon shugban kasar Uganda Idi Aminu Dada a tsakanin watan Augustan 1923 zuwa 1928,a cikin kabilar Kakwa dake kusa da lardin Arua na kusa da bakin ruwa dake kasar Uganda.Mahaifiyarsa tsohuwar unguwar-zoma ce ta gargajiya yayin da mahaifinsa kuma ya kasance tsohon jami’in ’yansandan Uganda.

Marigayin Idi Aminu Dada ya muli kasar Uganda ne tun daga 1971 zuwa 1979.

A lokacin mulkin Idi Amin a kasar Uganda ya fi mayar da hankali ne wajen nuna kabilanci,inda a wanan lokacin ya bada umarnin halaka daulolin Acholi da Lango na kasar da kuma sauran kabilu da yawan su ya tasamma 1,000 zuwa 3,000.

Marigayi Idi Amin ya shiga makarantar horas da soji ta Birtania a shekara ta 1964,inda wanan lokacin ya kai ga samun mukamin Lutanat.

Bayan da kasar Uganda ta sami yancin kanta a shekara ta 1962,Milton Obote,Friministan farko na Uganda ya daga darajar Idi Amin izuwa mukamin kaftin a shekara ta 1963 saboda irin biyayarsa.

Marigayi Idi Aminu Dada ya zama mukaddashin kwamandan sojin Uganda a shekara ta 1964.

A shekara ta 1965 an zargi Idi Amin da kuma Obote da laifuka na fasa kwaurin Gold da Coffee da kuma hauren-giwa daga cikin jamhuriyar Democradiyar Congo.Wannan dalili ne ma ya sanya shugaban kasa Fredrick Walugembe ya kafa kwamitin bincike na yan majalisar dokokin Uganda,da nufin bincika abinda ya faru.

A shekara ta 1962 sarki Buganada da aka fi sanni da sarki Freddie ya daga likafar Idi Amin izuwa mukamin janar kuma aka bashi mukamin shugaban hafsan sojin Uganda,tun daga wanan lokacin ne ya bada umarnin kame yan majalisar ministocin Uganda biyar tare da soke kundin tsarin mulkin kasar,nan take kuma ya nada kansa a matsayin shugaban kasar Uganda.

Tun daga wanan lokacin ne aka tilastawa sarki Freddie yin gudun hijira zuwa Birtania a shekara ta 1969,a wannan shekarar ne kuma rai yayi halinsa.

Shi kuwa Marigayi Idi Amin ba abinda ya sanya a gaba sai shigar da yan kabilarsa cikin aikin soji,wannan dalilin ne ma ya haifar da rashin fahitar juna tsakanin Obote farkon Priministan Uganda da marigayi Idi Amin.Obote ya mayar da martani wajen bada umarnin a yiwa Idi Amin daurin talala,kuma ya rasa mukamansa na soji.

A lokacin da Marigayi Idi Amin ya fahimci cewa Obote na shirin kama shi bisa zarginsa da laifuka na almbazaranci da dukiyar sojin Uganda,sai ya kifar da gwamnatinsa ta hanayr juyin mulki na soji a ranar 25, ga watan Janairun 1971,a lokacin da shi Obote ke halartar baban taron kungiyar kasahen CommonWealth a kasar Singapore.

Tun daga wanan lokacin ne marigayi Idi Amin ya fara kiran kansa shugaban kasa,kuma Field Mashal tsawon rayuwarsa.

Gwamnatin marigayi Idi Amin Dada nada alaka da kungiyar kwatar yancin Palasdinawa.

A watan Octoban 1978 kimanin al’ummar kasar Uganda 1,000 zuwa 5,000 suka rasa rayukan su zamanin mulkin marigayi Idi Amin da ake ganin mulki ne irin na kama karya,wannan dalili ne ya sanya kasashe da dama na duniya suka soke dukkanin wata dangantaka da gwamnatin Uganda.

A Shekarar dai ta 1978,gwamnatin Marigayi Idi Amin ta yi kokarin mamaye wasu yankuna na kasar Tanzania,to sai dai kuma a 1978 gwamnatin shugaba Julius Nyerere ta fatattaki Idi Amin daga Tanzania,kuma ta mamaye birnin kamfala da taimakon yan tawayen Uganda,inda nan take aka mayar da Obote kan mukaminsa.

Tun daga wanan lokaci ne Amin yayi gudun hijira zuwa kasar Libya,kafin daga bisani ya sami mafakar siyasa a kasar Saudi Arabia,inda can din ne kuma ya zauna matansa hudu har ya zuwa lokacin da ya koma ga mahalicin mu,bayan wata matsanaciyar rashin lafiya da ya fuskanta,kuma aka kwantar da shi a asibitin kwararru na sarki Faisal dake Saudiya.

A lokacin da marigayi Idi Amin ke cikin hali na tsananin rashin lafiya,uwargidansa ta roki shugaban kasar Uganda Yoweri Museven da ya baiwa Idi Amin damar komawa gida don ya mutu a gida,amman kuma hakan bai yiwu ba.

Ana dai yi jana’izar marigayi tsohon shugaban kasar ta Uganda Idi Amin Dada a kasar saudi Arabia a ranar 16 ga watan Augustan shekara ta 2003.

Marigayi Idi Amin ya zamanto mashahurin zakaran damben Uganda har ya zuwa shekara ta 1960.

Muna fata mai sauraron namu ya gamsu da wannan amsa.