Tarihin hotel ɗin Ranch da ke Kampal | Amsoshin takardunku | DW | 10.11.2008
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Amsoshin takardunku

Tarihin hotel ɗin Ranch da ke Kampal

Taƙaitaccen tarihin hotel ɗin Ranch dake Kampala a ƙasar Uganda

default

Tafkin Victoria na Uganda inda hatel ɗin 'Ranch' yake

Tambaya: Fatawarmu ta wannan makon ta fito daga hannun malam Nazifi Abdullahi daga Maiduguri a jihar Bornon tarayyar Najeriya. Malamin cewa ya yi, don Allah Deutsche Welle ku bani tarihin shahararren Hotel ɗin nan na ƙasar Uganada, wanda aka ce yana bakin tafkin victoriya.


Amsa: To shi dai wannan Hotel sunansa (Ranch on the lake), wato “Dausayin bakin teku” a Hausance, kuma kamar yadda malam Nazifi ya faɗi, katafaren Hotel ne a ƙasar Uganda. Duk da cewa ba a cikin maraya ya ke ba, to amma dai bai yi nisa da ita ba. Ɗaya daga cikin guraren da ‘yan yawon shaƙatawa suke son ziyarta a Uganda shi ne bakin tafkin Victoria, tafki mafi girma a nahiyar Afirka, kuma anan ne Dausayin bakin tuku yake. Allah ya albarkaci wannan wuri da tsuntsaye kala daban-daban kuma muna da tsirrai nau'i-nau'i. Alal haƙiƙa idan mutum ya je wannan wuri, zai tabbatarwa da kansa cewa, dausayi ne da ya tattara abubuwa waɗanda ba a ko'ina ake samunsu ba.

Nau'o'in halittun tsuntsaye daban-daban ita ce cikakkiyar alamar wannan wuri. Baƙi sukan zo don su huta ko su shaƙata ko don su gujewa hayaniyar cikin birnin kampala. “Dausayin bakin teku” kamar yadda sunansa ya nuna, wani dausayi ne na musamman dake tsakanin tsaunuka a bakin tafikin Victoria. Daga nan za ka iya hango tsaunuka a can bangaren yamma, a ɓangaren gabas kuwa, ruwan tafkin Victoria ne yake ta toroƙo. Har ila yau a “dausayin bakin teku” akwai ɗan tafki na kiwon kifi. Waɗannan kifaye suna jan hakalin tsuntsayen dake nan, inda suke zuwa suna yin kalaci da su.


“Dausayin bakin teku” a wani lokaci ma akan yi masa laƙabi da “Gidan tsuntsaye” Kasancewar a kodayaushe wannan wuri ba ya rabuwa da kukan tsuntsaye nau'i daban-daban.


Ga duk mutumin da ke son ziyartar wannan hotel, ko kuma neman wani ƙarin bayani, zai iya tuntuɓar jami'an hotel ɗin ta wannan lamabar waya; +256 412 44 774.