1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

060608 Deutsch-französische Beziehungen Geschichte

Böhm, Manfred (DW)June 9, 2008

Tuntuɓar juna tsakanin Jamus da Faransa na da dadaɗɗen tarihi.

https://p.dw.com/p/EGBK
Merkel da SarkozyHoto: AP

Tuntuɓar juna tsakanin Jamus da Faransa na da dadaɗɗen tarihi. A ƙoƙarin yin sulhu tsakani bayan yaƙin duniya na biyu ƙasashen biyu sun ƙulla yarjejeniyar Elysee a farkon shekarar 1963. Taruka sau biyu da ƙasashen ke gudanarwa tsakaninsu a kowace shekara na matsayin ma´aunin kyatatuwar dangantaku tsakanin al´ummominsu da kuma shugabanninsu.


"Mun yi ƙoƙarin nunawa Faransawa cewa muna iya zama maƙwabtan kirki kuma mun yi ƙoƙarin nuna musu cewa buƙatanmu ɗaya ne wato ƙarfafa dangantaka tsakanin Faransa da Jamus."


Waɗannan dai kalaman tsohon shugaban gwamnatin Jamus marigayi Konrad Adenauer kenan, bayan da shi da tsohon shugaban Faransa Charles de Gaulle sun sanya hannu kan yarjejeniyar dangantaka tsakanin Jamus da Faransa a ranar 22 ga watan Janerun shekarar 1963. Tun daga wannan lokaci dukkan gwamnatocin Jamus da Faransa ke jaddada nauyi na bai ɗaya dake kansu. Bayan ta kama mulki a shekara ta 2005 shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ita ma ta bayyana dangantaku tsakanin Jamus da Faransa kamar haka.


"Bisa la´akari da ƙazamin yaƙin da aka gwabza a da, abin mamaki ne da yanzu ƙasashen Jamus da Faransa ke tafiyar da hulɗa ta ƙut da ƙut tsakaninsu. Wannan dangantaka ba ta tsaya ga ´yan siyasa kaɗai ba, ta wanzu tsaknain al´ummomin ƙasashen biyu."


A kullum ana ganin cewa duk wani haɗin kai dake aiki tsakanin Jamus da Faransa na matsayin sharaɗin ci-gaban dukkan shirye-shiryen haɗe kan nahiyar Turai. Samun haka kuwa alhaki ne da ya rataye kan dukkan shugabannin ƙasashen biyu waɗanda suka shuɗe da waɗanda ke kan mulki. Ba a zamanin dukkan shugabannin ne aka samu wanzuwar kyawawan dangantaku tsakani ba. Alal misali a farkon shekarun 1990 lokacin da aka kwatanta Helmut Kohl a matsayin shugaban gwamnatin haɗewar Jamus, dangantaka tsakanin Jamus da Faransa ta yi tsami. Inda bayan rugujewar tarayyar Sobiet haɗe da sauyin taswirar siyasar nahiyar Turai, gwamnati a birnin Paris ta yi fargabar cewa Jamus zata sake mamaye fagen siyasa a wannan nahiya. Amma shugaban gwamnati Helmut Kohl ya ɗauki wani muhimmin mataki bisa manufar ɗinke wannan ɓaraka inda a cikin watan Oktoban shekarar 1995 ya gayyaci shugaba Jacques Chirac zuwa gidansa.


Kohl ya ce "Abin da muka sa a gaba shi ne ƙarfafa haɗin kai tsakanin Jamus da Faransa domin haka na zaman sharaɗin wanzuwar kyakkyawar abokantaka da zaman lafiya da kyakkyawar makoma ga nahiyar Turai gaba ki ɗaya."


To sai dai duk da haka dangantakar ta sake yin tsami bayan zaɓan Gerhard Schröder a muƙamin shugaban gwamnati a shekarar 1998. A ziyararsa ta farko zuwa fadar Elysee mista Schröder ya yi takatsantsan duk da farin cikin da ya nuna ga wannan ziyara.


Sai a lokacin yaƙin Iraqi dangantaka tsakanin ƙasashen biyu ta fara ingantuwa musamman saboda adawa da wannan yaƙi da Schröder da kuma Chirac suka nuna. Tun daga wannan lokaci aka ƙulla wata abokanta ta ƙut da ƙut tsakanin Schröder da Chirac.

A tsakanin Merkel da Sarkozy ana samun fahimtar juna. To sai dai duk da wata nasara ta bai ɗaya kamar amincewa da yarjejeniyar tarayyar Turai akwai wasu bambamce bambamce tsakani. Kamar shirin Sarkozy na kafa wata tarayyar ƙasashen yankin Tekun Bahar Rum, wanda ke shan suka daga ɓangaren Jamus. Shugabannin ƙasashen biyu sun sa cewa duk wani shirin haɗakar nahiyar Turai ba zai kai gaci ba sai tare da haɗin kai cikakken haɗin kai tsakanin Jamus da Faransa.