1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tarihin Barewa Collage

Yusuf BalaJanuary 6, 2016

A shekarar 1945 dalibai 25 da ake dauka a makarantar an ninka adadinsu ya zuwa 50. A shekarar 1949 an mai da kwalejin zuwa Zariya.

https://p.dw.com/p/1HVfI
Karte Nigeria Zaria Englisch/Deutsch

To ita dai wannan makaranta ta Barewa Collage a lokutan baya ana kiranta da sunaye da dama kama daga babbar kwalejin jihar Katsina ko Katsina Higher Collage da Kaduna Collage da Sakandaren Zariya yanzu kuma a ke kiranta Barewa Collage Zariya.

An kafa ta a karon farko da sunan Kwalejin horas da malamai ta Jihar Katsina a shekarar 1921 domin horas da malamai a lardin Arewacin Najeriya a lokacin Gwamna Janar Sir Hugh Clifford inda cikin muradan horan da malaman ke samu bai tsaya kawai ga koyon karatun littafi ba su koyar har da batun koyar da wasu dabiu masu kyau da za a gani a tare da su dan amfanin al'umma.

Bayan da bukatar neman karin ma'aikata ta tashi a Arewacin Najeriya dan cike guraben aikin gwamnati a wannan lokaci aka daga martabar wannan makaranta zuwa babbar kwalejin Katsina a shekarar 1929, da burin habaka samar da ma'aikata masu nagarta, a wannan lokaci ne a ka shigo da tsarin koyar da ilimin kimiya ta yadda dalibai za su bada gudunmawa a fannoni na fasaha da hada magunguna da kula da gandun daji da ayyukan gona da ma ayyukan kula da lafiya a Yaba.

A wannan shekara ce ta 1929 shirin maida kwalejin wani kebabben wuri da ma batun daga martabarta su zama daya da kwalejin ta Yaba aka aje maganar. Amma yanayi na ci gaba da aka samu a tsarin siyasar duniya da ma tattalin arziki a shekarar 1930 zuwa 1940 hakan ya sanya shugabannin mulkin mallaka da ke zama Turawa a wancan lokaci suka sauya manufa inda a shekarar 1935 aka amince da shirin mai da kwalejin Kaduna aka kuma aiwatar a shekarar 1937 zuwa 1938. Tun da fari dai garin na Zariya shi ne aka tsara cewa inda za a girka makarantar sai dai an fara aiwatar da harkokin makarantar a Kaduna.

A shekarar 1945 dalibai 25 da ake dauka a makarantar an ninka adadinsu ya zuwa 50. A shekarar 1949 an mai da kwalejin zuwa Zariya.

A lokacin da kwalejin ta koma Zariya an kira ta da Sakandaren Zariya bayan da wasu makarantun lardin suke bunkasa an daga martabarta zuwa Kwalejin gwamnati da ke Zariya. A shekarar 1971 ne aka kira ta BAREWA Collage kuma ta dauki sunan ne saboda yadda ta ke bunkasa cikin sauri tamkar barewa. Hakan kuma na zuwa ne adaidai lokacin da aka kafa gwamnati mai jihohi shida a yankin Arewacin na Najeriya.