1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tarihin Barack Obama

Yahouza, SadissouAugust 28, 2008

Taƙaitacen tarihin Barack Hussain Obama,ɗan takarar Jam´iyar Demokrate a zaɓen shugaban ƙasar Amurika.

https://p.dw.com/p/F6Bl
Barack Obama, dan takarar Jam´iyar DemokrateHoto: AP/DW


An aifi Barack Hussain Obama ranar 4 ga watan Oguster na shekara ta 1961 a birnin n Honolulu dake yankin Hawai a ƙasar Amurika.

Tun yana ɗan shekaru biyu da aihuwa iyayensa suka rabu, ya cigaba da zama tare da ma´aifiyarsa.

Ubansa musulmi ƙan kasar Kenya a nahiyar Afrika, ya bar Amurika bayan ya rabu da matarsa ba´amurika inda ya koma gida Kenya, ya kuma zama minister a cikin gwamnatin shugaban ƙasa na farko, wato Jomo Keniyatta, kamin Allah ya amshi ransa, a shekara ta 1982  a cikin haɗarin mota.

A lokacin da ya samu shekaru shida, har zuwa shekaru 10, Barack Obama ya bi ma´aifiyarsa  a ƙasar Indonesia inda suka yi zama na shekaru huɗu.

Sai a shekara ta 1971 ya komo Honolulu, inda ya ci gaba da karatu.

Yayi karatu  a jami´ar Californiya da kuma ta Columbiya  a birnin New York.

Bayan ya kamalla karatu, a jami´a, Obama ya fara aiki a matsayin jami´i, ta fannin lissafin kudi.

To saidai ba jima ba yana wannan aiki ya kuma koma ƙarin ilimi, inda a shekara ta 1991 ya fito da digrin digirgir ta fannin sharia´a.

Barack ya jima ya na kwaɗayin shida siyasa, amma sai a shekara ta 1996 haƙƙarsa ta cimma ruwa, inda karon farko a ka zaɓe shi a matsayin dan majalisar a mazaɓarsa ta yankin Ilinois.

A shekara ta 2004 ya shiga Majalisar Dokokin Amurika.

A tsawan watani 18 Barack Obama na fafatawa da matar tsofan shugaban ƙasar Amurika, wato Hilary Clinton domin samun tabaraki daga jam´iyar Demokrate don tsaya takara a zaɓen shugaban ƙasar Amurikar.

A wani matakin da wasu ke dangatawa da "rabbo rabbabe", babbu zato babu tammaha, Barack Obama ya kai gaci tare da kasa abikiyar hammayar tasa.

A duk tsawan wannan lokaci Obama ya bayyana kansa a matsayin gwarzo, duk da cewar da dama na masa zargin rashin ƙurrewa cikin  harakokin siyasa, idan aka kwatanta shi da Hilary Clinton, ko kuma da ɗan takara jam´iyar Republicain John Makain, mai shekaru 72  a duniya,wanda kuma ya laƙanci ƙabli da ba´adin siyasa, a ciki da wajen Amurika.  

Ta fannin rubuce rubuce,Barack Obama, ya rubuta littatafai guda biyu, inda a ɗaya daga cikin su, yayi tarihin rayuwar baƙƙaƙe a Amurika, tare da bayyana yadda a matsayinsa na baƙin ba´amurike ya gudanar da yarintarsa.

Barack Obama,na da aure da kuma ´yaya,´yan mata guda biyu.

Abinda Amurika da sauran al´umomin duniya suka zuba idio su gani a halin yanzu shine ko Amurika ƙasar da ta fi ƙarfin tattalin arziki a duniya, za ta sami a karon farko cikin tarihi, shugaba baƙar fata ? Sai mu dakaci ranar 4 ga watan November na wannan shekara.