Tarayyar Turai: Tusk ya yi tazarce | BATUTUWA | DW | 09.03.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

BATUTUWA

Tarayyar Turai: Tusk ya yi tazarce

Kungiyar Tarayyar Turai ta tabbatar da Donald Tusk a matsayin wadda zai ci gaba da jagorantar Majalisar Hadin kan Turai karo na biyu, bayan da aka sake zaben shi.

Zababben shugaban Majalisar Hadin kan Turai Donald Tusk

Zababben shugaban Majalisar Hadin kan Turai Donald Tusk

An dai sake zaben Donald Tuks din ne a yayin taron da kungiyar Tarayyar Turan ta gudanar a birnin Brussels na Kasar Beljiyam. Duk da matsananciyar adawa da Tusk din ya fuskanta daga kasarsa ta Poland da ke masa kallon dan adawar gwamnati, inda har ta kai ga tura sunan wani dan majalisar kasar domin maye gurbin Tusk din, ya kai ga samun nasarar lashe zaben da ya ba shi damar ci gaba da rike mukamin na shugaban Majalisar Hadin kan Turai a karo na biyu, wanda kuma zai ba shi damar jan ragamar majalisar har na tsawon shekaru biyu da rabi masu zuwa. Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel na daga cikin wadanda suka mara wa Donald Tusk baya wajan samun nasarar lashe zaben daya daga cikin manyan mukamai a kungiyar Tarayyar Turan, da aka gudanar a wannan Alhamis din a birnin Brussels, ta kuma ce:

"Ina ganin zabensa a matsayin wani gagarumin cigaba ne ga daukacin kungiyar EU, zan kuma cigaba da bashi hadin kai da goyon baya, sannan kuma ficewar Birtaniya daga kungiyar wani lamari ne da ya kamata ya zama darasi tare da tuni a gare mu, duk da cewa akwai dalilai da dama da suka taka muhimmiyar rawa kan ficewar Birataniyan."

Kalubale mai tarin yawa:

Zauren taron kungiyar Tarayyar Turai EU

Zauren taron kungiyar Tarayyar Turai EU

Zaben na Tusk dai a karo na biyu na cike da kalubale duba da yanayin da Turan ke ciki a yanzu musamman ma dangane da batun 'yan gudun hijira, da ke yi mata kallon tudun mun tsira tare da kwarara cikinta a koda yaushe. A halin yanzu dai kungiyar Tarayyar Turan na zaman wani dandalin hana 'yan gudun hijira ko masu neman mafaka shiga kasashen Turai duba da yadda kasar Hangary ta ke tsare 'yan gudun hijira a wani sansani da ta tanada. A  shekarar da ta gabata ne kungiyar Tarayyar Turan ta kargame magamar Balkan, da ke zaman wata hanya da 'yan gudun hijirar ke bi dominn shiga nahiyar Turai, kana ta kulla wata yarjejeniya tsakaninta da mahukuntan Ankara, inda suka amince da mayar da sababbin 'yan gudun hijirar kasar Siriya da ke Girka zuwa kasar Turkiyya. Jim kadan bayan fara aiki da wannan yarjejeniya dai canji ya fara bayyana karara, inda adadin 'yan gudun hijirar da ke kwarara cikin kasashen Turan ya fara raguwa. A cewar masharhanta wannan mataki na nuna aniyar kungiyar Tarayyar Turan karara na kyamar 'yan gudun hijira. Abin jira a gani shi ne rawar da Tusk din zai taka bayan sake zabensa a karo na biyu a matsayin shugaban Majalisar Hadin kan Turan, idan aka yi la'akari da yadda a baya kawunan kasashen Turan ya rabu musamman ma a kan batun na 'yan gudun hijira.

Sauti da bidiyo akan labarin