1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Tara Ga Watan Nuwamba

A ranar tara ga watan nuwamban shekara ta 1989 ne dubbanin 'yan tsofuwar Jamus ta Gabas suka gabatar da matakinsu na rushe katangar Berlin lamarin da yayi jagora zuwa ga sake hadewar kasashen Jamus ta Gabas da Jamus ta yamma

Ranar tara ga watan nuwamba ta shiga kundin tarihin Jamus, saboda rana ce dake shaidar da faduwar katangar Berlin da kuma kawo canji ga siyasar duniya baki daya. Domin kuwa watanni goma sha daya bayan haka aka yi bikin sake hadewar kasar ta jamus a daidai ranar uku ga watan oktoban shekarar 1990. Bugu da kari kuma tare da rushewar mulkin kama-karyar Jamus ta Gabas tsarin mulkin kwaminisanci ya gushe daga taswirar nahiyar Turai baki daya aka kuma kawo karshen zaman doya da manjan da aka yi tsawon shekaru masu tarin yawa ana fama da shi tsakanin kasashen gabaci da na yammacin duniya. Ita dai ranar tara ga watan nuwamba gaba daya tana taka muhimmiyar rawa a tarihin Jamus. Domin kuwa a irin wannan ranar ce a shekara ta 1918 Philipp Scheidemann dan jam’iyyar Socialdemocrats ta gabatar da jawabinsa na kafa janhuriya tare da kawo karshen mulkin mulukiyya karkashin sarkin sarakuna Wilhelm II. Bayan kafa wannan mulki na demokradiyya kasar ta Jamus ta sha fama da matsaloli, inda dukkan masu zazzafan ra’ayi na gurguzu da na mazan jiya suka shiga fafurukar murkushe wannan tsari. A daidai ranar tara ga watan nuwamban shekarar 1923 ‘yan jam’iyyar Nationalsocialist ta Hitler suka yi jerin gwano zuwa dandalin Felherrnhalle a birnin Munich. Shekaru goma bayan haka Hitler ya dare karagar mulkin Jamus sannan ya jefa duniya a cikin masifar yakin duniya na biyu. Amma fa kafin hakan ya faru sai da aka rika danne hakkin Yahudawan Jamus sannu a hankali, kafin a yi musu kisan kare dangi a shekarar 1942. A daidai ranar tara ga watan nuwaban 1938, jim kadan kafin barkewar yakin duniya na biyu an shiga cunna wa gidajen ibada da kantunan Yahudawa wuta a duk fadin kasar jamus, inda aka kashe 100 daga cikinsu sannan aka tesa keyar wasu dubu 26 zuwa sansanonin gwale-gwale a wannan rana. Wannan dai ya kasance matakin farko akan ta’asar kisan kare-dangin da ‘yan Nazinhitler suka aikata akan Yahudawa daga bisani. Ranar ta tara ga watan nuwamban 1938 ta zama mummunan tabo ga tarihin Jamus, a yayinda ita kuma tara ga nuwamban 1989 ta zama wata rana ta doki da murna ga Jamusawa saboda faduwar katangar da ta raba harabar kasarsu tsawon sama da shekaru arba’in. Tun kafin hakan ta faru dubban dubban al’umar Jamus ta Gabas suka nemi mafaka a ofishin jakadancin Jamus ta Yamma a kasar Hungary da sauran ofisoshin jakadancin kasar dake kasashen gabacin turai ‘yan kwaminis. Ala-tilas fadar mulki ta gabacin berlin ta ba da kai bori ya hau ga wannan matsin lamba domin ba wa al’umarta damar tafiye-tafiye. Amma wannan sanarwar ta bude kafar tsundummar dubbanin ‘yan gabacin Jamus zuwa Berlin, sannan ita kuma ranar tara ga watan nuwamban, a karo na hudu ta zama mai taka muhimmiyar rawa a tarihin Jamus.