Tanzaniya: Wasan motsa jiki don karfafa hazaka | Sauyi a Afirka | DW | 11.05.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Sauyi a Afirka

Tanzaniya: Wasan motsa jiki don karfafa hazaka

Mafarkin Nassoro Mkwesso da abokansa ya tabbata wajen tallafa wa matasa maza da mata su fara rayuwa mai ingaci a Tanzaniya.

Videostill AOM Africa on the Move Tansania Gemeinde Hilfe für Kinder mit Behinderung

Nassoro Mkwesso mai tallafa wa matasa

Wasu abokai matasa sun kirkiri wata cibiya a wani yanki na al'ummar Kigamboni a Dar-es-Salam babban birnin kasar Tanzaniya, kuma sun kirkiri cibiyar ne a shekara 2007 da nufin tallafa wa 'yan uwansu musamman matasa maza da mata su zamo masu dogaro da kansu ta fannin koyan sana'o'i dabam- dabam. Wadannan matasa dai sun taso cikin yanayin talauci inda suka samu tallafi daga al'ummar yankin, hakan ne ya karfafa masu gwiwa su ma su tallafa wa na kasa da su.

Nassoro Mkwesso shi ne matashin da ya jagoranci kafa cibiyar wadda aka yi wa lakabi da KCC, ya bayyana yadda rayuwa ta kasance masa kafin ya samu damar aiwatar da kudirin da ya sa gaba yana mai cewa.

"Na yi doguwar takardama sosai da 'yan gidanmu, hakan ne yasa na yanke shawarar barin gida lokacin ina dan kimanin shekaru 12. Na cigaba da yin gararanba tsawon watanni 12, kawai sai wata rana muka yi kacibis da mahaifiyata sai ta ce mun ya kamata in koma gida kuma zan iya yin duk abinda nike so."

Kusan shekaru takwas da suka gabata ne Mkwesso da abokansa suka kirkiro da cibiyar kuma wuri ne da ake koyar da sana'o'i dabam-dabam kyauta ga matasa. Ga misali 'yan mata za su iya koyan dinki madadin su zauna a gidaje suna jiran mijin aure kamar yadda Mkwesso ya kara da cewa.

"Manufar kafa wannan cibiya ta KCC ita ce don yaki da talauci da ba matasa maza da mata dama su gwada fasahar da Allah Ya yi musu ta hanyar ilimin da suke da shi da kuma ba mutanen da ba su samu damar yin karatu ba damar zuwa cibiyar ta KCC kyauta."

Videostill AOM Africa on the Move Tansania Gemeinde Hilfe für Kinder mit Behinderung

Daukar darasi a cibiyar KCC

Ana dai gudanar da kwasa-kwasai kowace shekara kama daga darussan na'ura mai kwakwalwa har ma da na Turanci.

Taimakon kai da kai don ci gaba

Ita dai wannan cibiya ta dogara ne kaco-kan kan irin gudummuwar da take samu wajen gudanar da al'amuran cikinta daga masu gudanar da ita da kuma kungiyoyin sa kai na kasa da kasa masu ba da tallafin jin kai.

Cibiyar dai takan tsugunar da yara masu gararanba a bakin tituna inji Mkwesso.

"Hakika muna so mu taimaka sosai amma ba mu da wadatattun kudi wadanda za mu iya daukar nauyin duka yaran. Kawo yanzu dai mun samu mun tsugunar da yara 12."

Zaman kashe wando dai tsakanin matasa yakan shafi har matasan birane ba ma karkara kadai ba. A kokarin wannan cibiya na tallafa wa matasa a karshen shekara 2014, rashin aikin yi ya ragu da kashi 15 cikin 100 a kasar Tanzaniya kuma sun sha alwashin ganin sun cigaba da karfafa gwiwar matasa don zamowa masu dogaro da kai.

Sauti da bidiyo akan labarin