1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tanttanawa tsakanin tawagogin Korea ta Arewa da ta Kudu

June 8, 2007
https://p.dw.com/p/BuJW

Tawagogin sojojin Korea, da maƙwabciyar ta Korea ta kudu, sun shiga sabuwar tanttanawa, kwana ɗaya bayan da Korea ta Arewan, ta yi gwajin harba makamai masu lizami.

Tantanawa tsakanin ɓangarorin 2 ta katse, yau da shekara ɗaya, sai a baya-bayan nan, hukumomin Pyong Yang da na Seoul, su ka cimma daidaito, akan wajibcin komawa teberin shawarwari ,da zumar kai ga zaman lahia mai ɗorewa.

Ƙasar Amurika, ta yi tur da wannan gwaji, da ta ɗauka tamkar matakin da kan iya maida hannun agogo baya, a tantanawar da ake, game da rikicin makaman nuklear Korea ta Arewa.

Kakakin gwamnatin Amurika a kan wannan batu,Gordon Johdroe, ya kira ga Korea ta Arewa, ta dakatar da harba makaman cikin gaggawa.