Tantannawar Bush da Denis Sassou N´guesso
June 5, 2006A jiya ne shugaba Georges Bush na Amurika, ya gana da takwaran sa, na ƙasar Kongo, bugu da ƙari shugaban ƙungiyar tarayya Afrika, Denis Sassou N´guesso.
A wannan ganawa da ta gudana a fadar White House, Georges Bush ,da Denis Sassou N´guesso, sun yi masanyar ra´ayoyi, a game da rikici daban-daban da ke cigaba da ɓarkewa a wasu sassa na Afrika, kamar Janhuriya Demokradiyar Kongo, da yankin Darfour na ƙasar Soudan.
Shugaba Bush yayi yabo da jinjina damste ga baƙon na sa, a dangane da kaukawar rawar da ya taka, a yarjejeniyar da aka rattaba hannu kanta, tsakanin yan Tawayen Darfour da gwamnati Sudan, a birnin Abuja na Tarayya Nigeria.
Kazalika, sun cimma daidaito a kan wajibcin aika tawagar shiga tsakani ta Majalisar Ɗinkin Dunia, cikin gaggawa a wannan yanki, domin tabbatar da yarjejeniyar.
Ta wannan fannin nema, wata tawagar komitin sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniyar, ta fara ziyara aiki a ƙasar Sudan yau lahadi.
Wannan rangadi na kwanaki 9, zai kai tawagar zuwa ƙasashe 4, da su ka haɗa da Sudan, Ethiopia Tchaad, da Jamhuriya Demokradiyar Kongo.
A dangane da cutar Aids kuma, magabatan 2, sun yi masanyar ra´yoyyin a kann matakan yaƙar ta, a nahiyar Afrika.
Sannan a ɗaya hanun, Bush ya yabawa yadda hukumomin Kongo, su ka tashi tsayin daka, wanda a sakamakon hakan ƙasar ta zama ɗaya daga ƙasashen Afrika, da a ka samu ci gaba a yaƙar cutar kabari sallamu alaikum.
Kazalika tawagogin 2, sun tantana, a game da yaƙi da ta´adanci, da kuma haɓaka tattalin arzikin nahiyar Afrika.
Denis Sassou N´guesso, ya bayana takwaran sa cewar ya samu gayyata, daga shugaban ƙasar Rasha Vladmir Poutine, domin halartar taron ƙungiyar ƙasashen G8, wata mai zuwa a birnin Saint -Petesburg na ƙasar Rasha.