Tantance wadanda harin Brussels ya shafa | Labarai | DW | 25.03.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tantance wadanda harin Brussels ya shafa

Yayin da ake ci gaba da bincike kan harin da aka kai a birnin Brussels na kasar Beljiyam, an gano cewa akwai Amirkawa da dan kasar China a cikin wadanda harin ya rutsa da su.

Belgien Brüssel John Kerry bei Charles Michel

John Kerry da Charles Michel na Beljiyam

Wannan batu dai na zuwa ne a yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike kan harin da ya yi sanadiyar rasuwar mutane sama da 30 tare kuma da raunata wasu masu yawa. Sakataren harkokin wajen Amirka John Kerry ya bayyana kansa a matsayin "mazaunin Brussels" a wani bangare na nuna alhininsa kan harin ta'addanci da aka kai a kasar ta Beljiyam a ranar Talata. Kerry ya bayyana haka ne a yayin ziyararsa da ya kai Beljiyam din, inda ya mika sakon jajantawa daga Shugaba Barack Obama na Amirkan ga Amirkawa biyu da daukacin al'ummar kasar ta Beljiyam da ma wasu kasashe da hadarin ya rutsa da su. Ita ma kasar China ta bayyana cewa cikin wadanda hadarin ya rutsa da su akwai dan kasarta guda, kamar yadda ofishin jakadancin kasar ya nunar. Mutane 31 ne dai suka rasa rayukansu yayin da wasu 300 kuma suka jikkata yayin wannan hari da tuni kungiyar 'yan ta'addan IS da ke neman ta addabi duniya baki daya ta dauki alhakin kai wa.