Tantanawa tsakanin tawagogin kasar Tchad da na Bankin Dunia a kan batun man Petur | Labarai | DW | 31.01.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tantanawa tsakanin tawagogin kasar Tchad da na Bankin Dunia a kan batun man Petur

Tawagogin bankin Dunia, da na gwamnatin kasar Tchad, na ci gaba da ganawa, a birnin Paris na kasar Faransa ,da zuma warware takkadamar da ta kunno kai,tsakanin su, a game da batun albarkatun man petur.

Ministan kuddi na Tchadi da ke hallartar wannan taro ya bayyana wa manema labarai cewa, babban burin da su ka sa gaba, shine ba kussanto ra` ayoyin bankin dunia da na gwamnatinTchadi ,a dangane da passalin kashe albarkatun man Petur na kasar Tchadin.

A kwanakin baya ne, shugaba Idriss Deby, ya yanke shawara saba alkawuran da ya sa hannu a kai tare da Bankin Dunia, a game da batun kassafin kuddaden albarkatu mai.

A sakamakon wannan mataki, Bankin Dunia ta matse bakin aljihun ta, ta hanyar kin zuba kudaden tallafi ga Tchad, kuma ta sa takunkumi ga dukkan kudaden da hukumomin kasar su ka mallaka, a bankunan Engla.