Tantanawa tsakanin shugaban hukumar Palestinawa da ministan tsaron Isra´ila | Labarai | DW | 16.11.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tantanawa tsakanin shugaban hukumar Palestinawa da ministan tsaron Isra´ila

A gefe daya, na taron birninTunis, an yi ganawa tsakanin shugaban hukumar Palestinawa Mahamud Abbas da minidtan tsaron Isra´ila Sylvan Shalom.

Wannan ganawa, itace ta farko da magaban 2, su ka yi, tun watan yuni da ya wuce.

Babban batun da su ka tantana akai, ya shafi zaman lahia a yankin gabas ta tsakiya, mussamn rikici da ya ki ci, ya ki cenyewa tsakanin Isra´la da Palestinu.

Abbas da Shalom, sun bayyana gamsuwa a game da yarjejeniyar da a ka kulla shekara jiya,ta inganta zirga zirga ta hanyar mashigar Raffah, bisa jagorancin sakatariyar harakokin wajen Amurika Kondalisa Rice.

Ministan tsaron Isra´ila, ya gayyaci Abbas, da ya tsawrara mattakan yaki da kungiyoyin ta´adanci na Hamas da Jihadil Islami, masu mayar da hannun agogo baya a yunkurin cimma zaman lahia a wannan yanki.