1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tantanawa tsakanin Saban Praministan Cote D´Ivoire da Jam´iyu siyasa da yan tawaye

December 12, 2005
https://p.dw.com/p/BvGj

Saban Praministan kasar Cote D´Ivoire, Charles Konnan Banny, ya fara ganawa da bangarori daban daban na siyasa, da yan tawaye ,domin girka sabuwar gwamnati.

A daya ya gana da shugaban kungiyar tarayya Afriak Olesegun Obasanjo, da kuma Tabon Mbeki na Afrika ta kudu, da ke shiga tsakaninrikicin kasar Cote D´Ivoire.

A wani taron manema labarai na hadi gwiwa da yayi da shuagabnAfrika ta kudu Charkls Konan Bany ya bayana cewa ya na kwattata zaton cimma nasara inganttata a wannan yauni da aka dora masa ta la´akari da yada ya samu goyabn dukan bangarori masu gaba da juna da kuma al´ummar kasa.

Kafofin sadarwa a kasar sun ruwaito cewa babban cikas da saban praministan zai fara fuskanta, shine na nada ministocin kudi da na tsaro.