Tantanawa tsakanin Hamas da Russia | Labarai | DW | 04.03.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tantanawa tsakanin Hamas da Russia

A birnin Mosco a na ci gaba da tantanawar da aka fara jiya , tsakanin tawagar Hamas da ta Rasha.

Maƙasudin wannan haɗuwa, da shugaban ƙasar Rasha Vladmir Poutin ya gayyata, ta jiɓanci neman matakan daidaita al´ammura, tsakanin Hamas da ƙasashen Turai, da kuma Amurika, a game da rikicin gabas ta tsakiya.

Tawagar Hamas, ta yi tsawuyar gwamen jaki,ga buƙatocin Amurika da ƙasashen turai, na cewar ƙungiyar, ta kwance damara yaƙi, ta amince da Isreala ,ta kuma, hau tebrin shawara , da hukumomi wannan ƙasa, don warware rikicin cikin ruwan sanhi.

Ya zuwa yanzu babu , babu wani abun a zo gani da a ka cimma a wannan zaman taro.

A yayi da Rasha , ke jaddada kira ga Hamas, na ta amince da buƙatocin ƙasashe masu shiga tsakani, shugaban tawagar ƙungiyar Hamas, Khalid Michael, ya maida martani da cewa, shariɗin amincewa da wannan buƙatoci shine, na fitar Israela kwata kwata, daga yankunan Palestinawa, da kuma dakatar da hare haren da ta ke kaiwa, ga al´ummomin Palestinu.

Saidai Khalid Michael, ya bayyana yiwuwar tsagaita wuta, ta wani ɗan lokaci, kamar yada yarjejeniyar da ɓangarori ta tanada a watan Juli na shekara da ta gabata.

Shugaban ƙasar Rasha, yayi hira ta waiyar talho, da shugabar gwamnatin Jamus, Angeller Merkel, domin sanar da ita halin da ake ciki, a wanan tantanawa.