Tana kasa tana dabo game da zaben shugaban kasa a Mexico | Labarai | DW | 08.08.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tana kasa tana dabo game da zaben shugaban kasa a Mexico

Shugaban jam´iyyar masu sassucin ra´ayi a Mexico, wato Manuel Lopez Obrador ya jagoranci wata zanga zanga, don neman sake kidaya kuri´un zaben shugaban kasa, da bai samu nasara ba, da yar karamar tazara.

Zanga Zangar, wacce aka gudanar da ita a kofar babbar kotun zabe ta kasar, ta samu halarcin dubbannin magoya bayan dan takarar neman shugabancin kasar ne, wato Mr Manuel Lopez.

Wannan zanga zanga dai tazo ne kwanaki biyu, bayan babbar kotun zabe ta kasar tace zata sake kidaya kashi 9 cikin dari ne na kuri´un zaben da aka kada, amma ba gaba dayan su ba kamar yadda dan takarar yake neman da ayi.

Zaben shugaban kasar da aka gudanar a ranar 2 ga watan yuli na wannan shekara, Mr Felipe Calderon na jam´iyyar masu ra´ayin mazan jiya ne ya lashe zaben da yar karamar tazara, akan abokin karawar tasa daga jamiyyar masu sassaucin ra´ayin.

Ya zuwa yanzu dai kafafen yada labaru sun rawaito Mr Manuel Lopez , na gargadin babbar kotun zaben kasar da cewa matukar bata sake kidaya kuri´un zaben bakin dayan su ba , to duk abin da ya biyo baya ita ta saya.