1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tana kasa tana dabo a game da tsaro a Srilanka

Yan tawayen kungiyyar Timil Tiger na kasar Srilanka sun halaka jami´an yan sandan shida.

Hakan ya biyo bayan tashin wani bom ne da yan tawayen suka yi, a yankin Batticaloa.

Wannan hari a cewar rahotanni yazo ne kwana daya bayan gwamnatin kasar ta bayar da sanarwar karbar tallafi daga kasashen waje da zuka tasamma dalar Amurka billiyan 4 da digo 5.

Kasashen da suka bayar da wannan tallafi sun gargadi mahukuntan na Srilanka yin sulhu da yan tawayen , in ba haka ba kuma su dakatar da tallafin da suke bawa kasar.

Wannan dai rikici dake tsakanin bangarorin biyu, an kiyasta cewa yayi yayi ajalin mutane sama da dubu sittin tun daga shekara ta 1972 kawo yanzu.