1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Tallafi ga Afrika ya dau hankalin jaridun Jamus

Batun tallafin kasashen Afirka ga yankin Sahel masu fama da matsalar yunwa da yaki suka dauki hankalin jaridun Jamus a wannan makon

A sharhin da ta rubuta mai taken taimako daga Afirka, jaridar Neue Zürcher Zeitung ta ruwaito shugaban hukumar tarayyar Afirka Moussa Faki Mahamat da zargin kasashe mambobin kungiyar AU da rashin taimakawa kasashen da ke fama da masifar yunwa, inda ya soki shugabannin Afirka da rashin shawo kan matsalar ta yunwa a kasashen kamar Somaliya da Sudan ta Kudu da kuma wasu yankuna na Najeriya.

Ita ko jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung a nata cewa ta yi kasashen kungiyar G5 Sahel da suka hada da Burkina Faso da Mali da Mauritaniya da Nijar da kuma Chad wadanda a ranar 6 ga watan Fabrairu na wannan shekara suka kulla kawance samar da rundunar hadin guiwa ta yaki da ta'addanci da dukkan nau'o'i na fasakauri a kan iyakokinsu. Jaridar ta ce kudurin kungiyar tarayyar Turai na bada gudunmawar Euro miliyan 50 a matsayin tallafi ga rundunar sako ne a baiyane ga Afirka da ma gamaiyar kasa da kasa. Sako ne kuma musamman ga kungiyoyin ‘yan ta'adda da masu fasakauri cewa an kuduri aniyar sa kafar wando guda da su.

Jaridar Der Tagesspiegel  a nata sharhin cewa ta yi mukaddashin shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo na cewa duk mai son ya taimaka wa Afirka to dole ya toshe hanyoyin shiga da kudi kasashen EU ta haramtattun hanyoyi. Jaridar ta ce kungiyar kasashe masu arzikin masana'antu ta G20 a karkashin jagorancin shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel a wannan karo ta sha yabo saboda sanya batun habaka nahiyar Afirka a sahun gaba na ajandarta. Jaridar ta ce muhimmin mataki na farko shi ne gaggauta fara aiki da sabbin ka'idojin EU na yaki da halasta kudin haramun.