1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taliban ta dauki alhakin harin Kabul

January 21, 2018

Taliban ta ce ita ce ta kaddama da hari kan babban Otel na Kabul da ya salwantar da rayuka da raunata wasu ciki har da baki da suka kasance a wajen.

https://p.dw.com/p/2rFiO
Afghanistan - Sicherheitskräfte nach Schüssen am Intercontinental Hotel in Kabul
Hoto: Reuters/M. Ismail

Kungiyar Taliban ta dauki alhakin harin da aka kaddamar a Otel din Intercontinental na Kabul babban birnin kasar Afghanistan, inda akalla mutum shida suka mutu wasu bakwai kuwa suka jikkata. Kungiyar ta ce mayakanta biyar ne suka kaddamar da harin da ya dauki sa'o'i masu yawa.

Ma'aikatar harkokin cikin gidan kasar ta Afghanistan ta ce an kwato Otel din daga hannun 'yan bindigar, sai dai wasu rahotannin sun ce an ji kara mai karfi a wajen.  Kakakin ma'aikatar Najib Danish, ya ce an ceto mutane 153 ciki har da baki 'yan kasashen waje su 41.

A ranar Alhamis ne dai ofishin jakadancin Amirka da ke birnin na Kabul, ya ja kunnen Amirkawa kan yiwuwar iya fuskantar hare-hare a musamman Otel Otel a birnin.