1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Talauci a Duniya

Abba BashirSeptember 18, 2006

Yawan masu fama da talauci a Duniya

https://p.dw.com/p/BvVF
Almajirai
AlmajiraiHoto: DW

Jama’a masu sauraronmu assalamu alaikum, barkammu da wannan lokaci, barkammu kuma da sake saduwa da ku a cikin wani sabon shirin na amsoshin takardunku,shirin da yake amsa tambayoyin da ku masu sauraro kukan aikomana.

Tambaya:Fatawarmu ta wannan makon ta fito daga hannun,malama Habiba Dayyabu ta garin Biu, dake Jihar Borno a Tarayyar Najeriya.

Malamar cewa ta yi; Shin, Mutane nawa ne suke rayuwa cikin matsanancin talauci a fadin wannan Duniya?

Amsa: To kamar dai yadda wani rahoto ya bayyanar daga sashen yada labaru na Bankin Duniya, ya nunar da cewa, sama da Mutane Miliyan Dubu ne (1,000,000,000) ke rayuwa a cikin matsananciyar fatara da talauci a fadin wannan Duniya tamu. Kuma an bayyana talauci da cewa, rayuwa ce da Dan’adam yake yi a kasa da dala daya ta Amurka(US$1) a kowacce rana. Kuma dala daya ta Amurka shine kimanin Naira N120 kenan a kudin Najeriya.

Matsakaicin Talauci kuwa inji Bankin Duniya, shine rayuwa akan dala daya zuwa dala biyu ta Amurka (US$1 - $2) a kowacce rana. Wato kimanin Naira N120 – 240 kenan a kudin Najeriya.

A gabaki dayan magana dai, an tabbatar da cewa, fiye da rabin Al’ummar Duniya suna rayuwa ne a cikin talauci, wato ma’ana sama da mutane Miliyan dubu uku (3,000,000,000) suna rayuwa ne a kasa da dala biyu (US$2) ta Amurka.

Akwai abubuwa guda biyar da suke kara tabbatar da cewa,da yawa daga cikin Al’ummar Duniya suna cikin halin kaka-na-kayi. Wadannan abubuwa kuwa sune;

Na daya: A kowacce shekara, sama da Mutane Miliyan takwas (8,000,000) ne suke mutuwa, saboda kawai tsananin talaucin da ya sa baza su iya rayuwa a doron kasa ba.

Na biyu: Fiye da Mutani Miliyan dari takwas (800,000,000) ne, suke kwana da yunwa a kowacce ranar Allah.

Na uku: gaba daya idan aka tattara tattalin arziki da kadarori na kasashe arba’in-da-takwas (48) mafiya talauci a Duniya, to gabadayan dukiyar tasu bata kai yawan ta Mutane uku (3) mafiya arziki a Duniya ba.

Na hudu: Yara dubu talatin ne, suke mutuwa kowacce ranar Allah, sakamakon yunwa da kananan cututtukan da za’a iya maganin su.

Na biyar: Yara miliyan shida ne suke mutuwa kafin su cika shekaru biyar a Duniya, saboda rashin samun abinci mai gina jiki.

Duk wadannan bayanai sun fito ne daga ofishin Bankin Duniya, mai kula da kididdigar yanayin talaucin da Al’ummar Duniya suke ciki. Kuma duk mai neman karin bayani a game da talauci a gasashe daban-daban na Duniya, sai ya duba shafin Bankin Duniya a yanar-gizo, wato “internet’’

Mai suna "PovertyNet''. Kuma ida Mutum yana da bukatar sanin yadda Bankin Duniya ya fitar da wannan kididdiga ta yanayin talaucin da Al’ummar Duniya suke ciki, sai a duba shafin yanar-gizo mai suna "PovcalNet''.