Takunkumin Amurka akan Sudan | Siyasa | DW | 30.05.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Takunkumin Amurka akan Sudan

Amurka na da niyyar tsaurara matakan takunkumi akan Sudan

George Bush

George Bush

A cikin jawabin da ya bayar shugaba George W. Bush ya ce yana wa al’umar Darfur alkawarin cewar Amurka ba zata yi watsi da wannan rikici dake daukar hankalin duniya baki daya ba. Shugaban na Amurka ya gabatar da bayanai akan wasu tsauraran matakan takunkumin karya tattalin arziki akan kasar Sudan, abin da ya hada har waharamcin cinikin wasu kayayyakin kamfanonin gwamnati. Bush ya ci gaba da cewar:

“A baya ga haka matakanmu zasu shafi wasu daidaikun mutane, wadanda ke da alhakin ta’asar dake wanzuwa. Matakan na takunkumi zasu taimaka mu mayar da wadannan mutane saniyar ware ta hanyar hana musu kafar kutsawa kasuwanninmu na kudi da gudanar da huldar ciniki da ‘yan kasar Amurka tare da janyo hankalin duniya zuwa ga miyagun laifukansu.”

Tun misalin makonni shida da suka wuce ne wannan shiri na takunkumi ke kan teburin shugaba George W. Bush. A wancan lokaci, a watan afrilun da ya gabata, shugaban ya dage shawarar sakamakon sa baki da sakatare janar na MDD Ban Ki Moon yayi, domin neman karin lokacin shawarwari da gwamnatin kasar Sudan. Amma babu wata nasarar da aka cimma in ji George Bush:

“A makonnin da suka wuce shugaba Bashir ya ci gaba da bin tsaffin manufofinsa da aka sani, inda a bangare guda yake alkawarin ba da hadin kai a yayinda a daya bangaren kuma yake hana ruwa gudu wajen cimma tudun dafawa.”

A takaice shugaba Al-bashir bai rungumi alhakin dake kansa da hannu biyu-biyu ba. Amma duk da haka shugaba George W. Bush ya ce zai ci gaba da neman bakin zaren warware rikicin lardin na Darfur a siyasance. Shugaban na Amurka ya kara da yin kira ga fadar mulki ta Khartoum da ta amince da tsugunar da sojan kiyaye zaman lafiya na MDD a lardin, wanda rikicinsa yayi sanadiyyar rayukan mutane sama da dbu 200. Kazalika ya ce ya nema daga sakatariyar harkokin waje Condoleeza Rice da tayi hadin kai da Birtaniya da sauran kawayen Amurka wajen zayyana sabon kudurin MDD akan Darfur domin kara matsin lamba ta kasa da kasa akasn Sudan. Kawo yanzun dai kasar China ce ke adawa da duk wani mataki na takunkumi saboda kakkarfar huldar ciniki dake tsakaninta da Sudan. Amma Bush yayi kira ga dukkan kafofi na kasa da kasa da su yi bakin kokaerinsu wajen dakatar da kisan kiyashin dake wanzuwa a lardin Darfur.

Bush ya ce:al’umar yankin na bukatar taimako sun kuma cancanci samun taimakon. A saboda haka nike kira ga MDD da KTA da ma duniya baki daya da su yi fatali da duk wani yunkuri na hana wamnzuwar zaman lafiya a Darfur da sauran sassa na kasar Sudan.