1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Takunkumi akan jami'an kasar Iran

September 30, 2010

Amirka ta sanya takunkumi akan man'yan jamian Iran su takwas bisa zargin take hakkin bil'adama

https://p.dw.com/p/PQMK
Hoto: WILLIAM B. PLOWMAN, MEET THE PRESS

Shugaban Amirka Barak Obama ya bayar da umarnin sanya takunkumi akan wasu manyan jami'an gwamnatin Iran guda takwas bisa zargin irin rawar da suka taka wajen shawo kan zanga - zangar da ta gudana domin nuna adawa da sakamakon zabukan kasar na shekara ta 2009. Umarnin - na shugaba Obama dai, yana nufin haramtawa jami'an taba kadarorin su da ke Amirka.

Daga cikin wadanda lamarin ya shafa - harda babban kwamandan rundunar juyin - juya - halin kasar Muhammad Ali Ja'afari, da ministan kula da harkokin leken asiri a kasar ta Iran, kana da babban mai gabatar da ka'ra na gwamnati. Sai kuma mukaddashin shugaban rundunar 'yan sandan kasar da kuma tsohon babban mai gabatar da ka'ra Saeed Mortazavi. Hakanan hukumomin na Amirka za su haramtawa man'yan jami'an takwas takardar izinin shiga kasar su.

A lokacin wani taron manema labaran da ta gudanar, sakatariyar kula da harkokin wajen Amirka Hillary Clinton, ta ce wannan ne karon farko da gwamnatin Amirka ke sanyawa jami'an kasar Iran takunkumi bisa abinda ya shafi take hakkin bil'adama.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh

Edita : Umaru Aliyu