Takun saƙa tsakanin Amirka da Rasha | Labarai | DW | 29.06.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Takun saƙa tsakanin Amirka da Rasha

Amirka ta ce ta yi nasarar cafke jami'an Rasha waɗanda ke yin leƙen asiri a Amirka

default

Mutane 10 ne hukumomin Amirka suka tsare bisa zargin suna yiwa ƙasar Rasha leƙen asiri a ƙasar ta Amirka. Jami'an gwamnatin Amirkar suka ce nasarar cafke mutanen ya biyo bayan tsawon shekaru da dama da suka ɗauka ne suna sanya ido akan ayyukan su.

Hukumar leƙen asiri ta Amirka FBI ta yi da'awar bankaɗo wasu saƙonnin dake nuna cewar, akwai jami'an leƙen asirin da gwamnatin Rasha ta tura domin tsegunta mata yadda lamura ke tafiya a tsakanin masu faɗa a ji a cikin gwamnatin Amirka, da kuma miƙa mata bayanai game da batutuwa da dama, waɗanda suka haɗa da maƙaman ƙare dangin da Amirka ta mallaka, da shirin ƙayyade makamai na Amirka, kana da batun ƙasar Iran da kuma zaɓen shugaban ƙasar Amirkar daya gabata.

Sai dai kuma ma'aikatar kula da harkokin wajen ƙasar Rasha ta bayyana cewar, tana jiran samun bayani daga hukumomin na Amirka bisa tsare mutanen, inda kuma ta fitar da wata sanarwar dake ambata zarge zargen a matsayin waɗanda basu da tushe balle makama, tana mai ƙarawa da cewar, abin taƙaici ne daya zo kwanaki ƙalilan bayan ziyarar da shugaba Medvedev na Rasha ya kai zuwa birnin Washinton na Amirka a kwanakin baya bayannan.

Mawallafi : Saleh Umar saleh

Edita : Yahouza Sadisou