1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Take hakkin maneman labarai a nahiyar Afirka.

Leonard Vincent, shugaban reshen Afirka na kungiyar nan "Reporter Sans Frontiere" ta maneman labarai, ya yi fira da gidan rediyon Deutsche Welle, a kan matsa wa `yan jaridu lamba da hukumomin kasashen Afirka da dama ke yi.

Alamar kungiyar Reporter Sans Frontière.

Alamar kungiyar "Reporter Sans Frontière".

Tabarbarewar halin zaman lafiya a nahiyar Afirka, ita ce dai batun da ya fi ci wa masu sa ido kan al’amuran nahiyar tuwo a kwarya. Ban da kasadar barkewar yaki tsakanin wasu kasashen, kamarsu Habasha da Eritrea, akwai kuma angaza wa maneman labarai da ake ta kara yi a wasu kasashen na nahiyar Afirka. Matsalar dai tana ta kara muni ne a kusan duk inda aka waiwaya a nahiyar, kamar yadda Leonard Vincent, babban darektan reshen Afirka na kungiyar maneman labaran nan Reporter Sans Frontière ya bayyanar, a cikin wata fira da ya yi da sashen faransanci na nan gidan rediyon Deutsche Welle. Ban da tantance labarai da hukumomin kasashe da dama na nahiyar ke yi, inji darektan, akwai kuma wasu matsaloli:-

„Wato matsaloli ne masu kawo mana damuwa, duk da cewa dai, bas u ne mafi tsanani a nahiyar ta Afirka ba. Amma abin da ya fi bata mana rai shi ne yadda ake ta jefa maneman labarai a gidajen yari ba gaira ba dalili kamar dai a kasashen Eritrea da Habasha, inda a halin yanzu ake tsare da maneman labarai da dama, wadanda kuma ake yi musu zargin cin amanar kasa da kuma samun hannu a wasu laifuffuka kamarsu kisan gilla.“

Su ko maneman labarai, a ko’ina ma, kokarinsu ne samo tushen labarai, sahihi, don fadakad da jama’a kan yadda ababa ke wakana takamaimai a yankuna daban-daban na duniya. Amma a wasu wuraren, sun fi huskantar matsaloli wajen gudanad da aikinsu. Haka dai lamarin ke wakana a nahiyar Afirka. Sau da yawa kuma, ana jefa maneman labaran a kurkuku ne ba tare da `yan uwansu sun sami labarin halin da suke ciki ko kuma, inda ake tsare da su din ba. Ta hakan ne kuwa, a galibi, ake halakad da wasu daga cikinsu, su bace ma kamar sun yi layar zana, ba tare da `yan uwansu sun gano burbushinsu ba.

Akwai dai kasashe da dama na nahiyar, inda irin wadannan kashe-kashen gillan suka auku ga maneman labarai, yayin da suke gudanad da aikinsu, inji Leonard Vincent. Kamar dai yadda ya bayyanar:-

„Idan muka dauki kasar Mozanbique alal misali, abin ban takaici ne irin kisan wulakancin da aka yi wa dan jaridan nan Carlos Cardoso a cikin shekarar ta 2000. Wannan dai, babban abin kunya ne ba ga Mozambique din kadai ba, ga ma nahiyar ta Afirka baki daya. Ba za mu iya mantawa kuma da kisan gillar da aka yi wa Norbert Zongo ba (wani dan jaridar kasar Burkina Faso, da aka halaka a ran 13 ga watan Disamban shekarar 1998, yayin da yake gudanad da aikinsa a wani wuri mai nisan kimanin kilomita dari daga Ouagadougou), da kuma Deyda Haydara, darektan jaridar nan „Point“, wanda shi ma aka yi masa kisan gilla a ran 16 ga watan Disamban shekara ta 2004 a birnin Banjul na kasar Gambiya. Sai dai, a daura da kasashen Burkina da Gambiya, hukumar shari’a ta Mozambique ta tashi tsaye tana binciken batun, kuma ana samun ci gaba a wannan binciken, wajen tabbatad da ganin cewa, an nuna adalci.“