Takarar neman shugabancin kungiyar WTO | Siyasa | DW | 12.05.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Takarar neman shugabancin kungiyar WTO

A yanzu gwagwarmayar neman shugabancin kungiyar ciniki ta kasa da kasa ta kai kololuwarta, inda 'yan takara biyu suka rage, del Castillo daga kasar Uruguay da Pascal Lamy daga Kungiyar Tarayyar Turai

Dan takara del Castillo

Dan takara del Castillo

Bisa ga ra’ayin Carlos Perez del Castillo, abu mafi alheri shi ne a yi rabon alhaki daidai wa daida wajen tafiyar da wadannan muhimman kafofi na kasa da kasa. Ita dai kungiyar ciniki ta kasa da kasa da aka kafa ta a shekara ta 1995 domin ta maye gurbin kungiyar ciniki da kwasta da aka kafa a shekara ta 1947, an yi shekara da shekaru tana karkashin jagorancin kasashen Turai. A matsayinsa na tsofon wakilin kasar Uruguay a kungiyar cinikin ta kasa da kasa WTO, del Castillo mai shekaru 60 da haifuwa, ya sha shugabancin tarurrukan kungiyar. A halin da muke ciki yanzun takarar neman mukamin darekta-janar na kungiyar ta rage ne tsakaninsa da Pascal Lamy, tsofon kantoman ciniki na kungiyar tarayyar Turai, domin mayewa gurbin darekta-janar mai ci, Supachai Panitchpakdi, dan kasar Thailand, wanda wa’adin shugabancinsa zai kare a karshen watan agusta mai zuwa. Zagayen shawarwarin ciniki na Doha da aka shiga a shekara ta 2001, yana da nufin kara kyautata yanayin ciniki ne ta yadda zai amfanar da kasashe masu tasowa, in ji del Castillo. Ya ce ta la’akari da haka, nada wani darekta-janar daga rukunin kasashe masu tasowa, wanda ya san makama, zai taimaka wajen cimma nasarar wadannan shawarwari. Shi dai darekta-janar mai barin gado Supachai, shi ne wani dan rukunin kasashe masu tasowa na farko da aka nada domin shugabancin kungiyar ta WTO. An kayyade shugabancin akan wa’adin shekaru uku-uku tsakaninsa da Mike Moore dan kasar New Zealand domin magance wani mummunan sabanin da ya kusa ya kawo baraka tsakanin kasashen kungiyar a shekara ta 1999. Shi ma Pascal Lamy dan takarar kungiyar tarayyar Turai dake da shekaru 58 da haifuwa, ko da yake kasashen kungiyar ne suka nada shi takara, amma yana nuni da irin goyan bayan da ya rika bai wa kasashe masu tasowa a matsayinsa na kantoman kungiyar tarayyar Turai akan al’amuran taimakon raya kasa. Ya ce nadinsa akan wannan mukami zai zama kamar dai ci gaba ne akan abin da ya saba gudanarwa tsawon rayuwarsa, domin kuwa sai da yayi shekaru 30 yana mai kula da al’amuran ciniki da raya kasa a nahiyar Afrika da Asiya da kuma Latin Amerika. Tun a zagayen farko ne aka yi awon gaba da ‚yan takara guda biyu daga kasashen Brazil da Mauritius. Abin da ake tsoro a yanzu shi ne ka da a fuskanci wata sabuwar baraka tsakanin kasashe masu tasowa da kasashe masu ci gaban masana’antu a zagayen karshe na takarar neman shugabancin kungiyar ta WTO, saboda irin wannan ci gaba zai gurgunta a ayyukanta, bayan tafiyar hawainiyar da aka fuskanta, wacce ta hana ruwa gudu ga muhimman batutuwan da suka shafi al’amuran ciniki na kasa da kasa, a tsakanin sassan biyu a cikin watannin da suka wuce.