1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Takarar Atiku a zaɓen Tarayyar Najeriya

Halimatu AbbasAugust 15, 2010

Tsohon mataimakin shugaban Najeriya, ya bayyana niyyarsa ta tsayawa takara.

https://p.dw.com/p/OoIy
Atiku Abubakar. tsohon mataimakin shugaban Najeriya.Hoto: AP Photo

Tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana ƙudirinsa na tsayawa takarar shugaban ƙasa a zaɓen shekara ta 2011. Matakin na Atiku Abubakar ya zo ne a daidai lokacin da jam'iyyar PDP mai mulki ta bai wa shugaban ƙasa maici yanzu, Goodluck Jonathan damar shi ma ya tsaya takarar, duk kuwa da adawar da wasu 'yan siyasar arewancin ƙasar ke nunawa. A makon jiya ne dai jam'iyyar PDP mai mulki ta Buƙaci Atiku Abubakar wanda a da ya fice daga jam'iyyar, sakamakon saɓani da tsohon shugaba, Olusegun Obasanjo, da ya samu amincewar jam'iyyar daga jiharsa ta Adamawa kafin a karɓe shi.

Kanfanin dillancin labaran AFP ya rawaito tsohon mataimakin shugaban ƙasar na cewa, ya fito neman takarar shugaban ƙasar ne a jam'iyyar ta PDP, domin ci-gaban ƙasa. Kamar dai yadda shi ma ya sheda wa Deutsche Welle yau a Abuja.

Bayan Atiku Abubakar, sauran 'yan takara a wannan zaɓe daga arewacin ƙasar sun haɗa da tsoffin shugabanin mulkin soja, Ibrahim Babangida da kuma Muhammadu Buhari, wanda karo na uku kenan yake neman wannan muƙami.

Mawallafi: Babangida Jibril

Edita: Halima Balaraba Abbas