Takaitaccen tarihin rayuwar Boris Yetsin | Siyasa | DW | 24.04.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Takaitaccen tarihin rayuwar Boris Yetsin

Marigayi tsohon shugaban kasar Rasha Boris Jelsin

Marigayi tsohon shugaban kasar Rasha Boris Jelsin

Daya daga cikin siffofi da suka yi fice na tsohon shugaba Boris Yeltsin da zai dade ana tunawa da shi a tarihin Rasha shi ne wani hoto nasa tsaye a kan tanki inda yana jajirce da kuma bujirewa wani yunkurin juyin mulki da sojojin tsohuwar tarayyar Soviet suka shirya a wancan lokaci.

Boris Yeltsin wanda ya rasu a ranar Litinin 23 ga wannan watan na Aprilu yana da shekaru 76 a duniya, jamaá na tunawa da shi ta fuskoki daban daban.

Alal misali a yammcin Turai da Arewacin Amurka suna daukar Yeltsin a matsayin jagoran sauyi kuma jigon dimokradiya a kasar Rasha. P/M Shugaban Amurka George W Bush a wani sako da wata mai magana da yawun gwamnatin ta karanta a madadin sa, ya baiyana Yeltsin da cewa mutum ne wanda ya sadaukar da rayuwar sa ga cigaban kasar sa.

Ko da yake wasu na yiwa Yeltsin masa kallo a matsayin mazari baá san gaban ka ba, zaá dauki lokaci mai tsawo ana tunawa da rayuwar sa. Wasu na iya yaba masa saboda yanto kasar sa da kuma gabashin turai da yayi daga danniya na tarayyar Soviet. Bugu da kari shine kuma shugaban da ya kawo karshen yakin cacar baka. A waje guda kuwa wasu na sukar lamirin sa saboda shi ya jawo rushewar tarayyar Soviet.

A daya bangaren kuma wasu jamaár da dama na tunawa da badakalar mulkin da ya gudanar wadda ta daurewa cin hanci da rashawa gindi kana uwa uba da munanan laifuka.

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta baiyana Boris Yeltsin da cewa mutum ne jan gwarzo wanda ya tsaya tsayin daka wajen habaka cigaban domkradiya dana tattalin arziki a lokacin da Rasha cikin mawuyacin hali. tace Yeltsin mutum ne na kwarai wanda kuma ya karfafa dangantaka tsakanin Rasha da Jamus.

Boris Yeltsin wanda ya yi mulkin Rasha daga shekarar 1991 zuwa 1999 ya gabatar da wasu matakai na dimokradiya da suka hada da yancin fadin albakarcin baki da kuma zabe bisa tsarin jaiyu da dama. Ya kuma bude iyakokin kasar ga harkokin kasuwanci da shige da fice da kuma zuba jari daga kasashen ketare.

Sai dai kuma ga masu fafutukar kare hakkin bil Adama boris Yeltsin mutum ne wanda ya aikta mummunan tabargaza ta laifukan yaki bisa ga rashin imanin da ya nuna a yankin Chechnya.

A cikin watan Disamba na shekarar 1994 ya kaddamar da mummunan yaki a kan musulmi yan aware, wannan manufa ta sa ta, ta jawo hasarar rayukan dubban jamaá, kusan ma dai a wannan lokaci an yi raga raga da Grozny babban birnin Chechnya kafin sojojin na Rasha su janye a shekarar 1996.

Tsohon shugaban tarayyar Soviet Mikhail Gorbachev ya baiyana Boris Yeltsin a matsayin Mummunan kaddara. Yace Yeltsin ya yi ayyuka na alheri kuma ya tafka kurakurai munana.

An dai haifi Boris Yeltsin a ranar daya ga watan Fabrairu, shekarar 1931, a wani kauye dake tsakanin tsaunukan Ural. Bayan kammala karatun sa na injiniya ya yi aiki a wasu kamfanonin gine gine inda ya rike mukamai da dama. A shekarar 1975 aka nada shi mukamin sakatare janar na gundumar Sverdlovski. Ya shahara a wajejan shekarar 1980 bisa basira da hangen nesa da ya nuna a jagorancin jamíyar sa.

A ranar 18 ga watan Augusta na shekarar 1991 wasu sojoji yan takife suka yi yunkurin kawar da Gorbachev daka karagar mulki, a nan ne Boris Yeltsin ya yi kundunbala ya mike a kan wata tankar yaki ta soji a kofar fadar gwamnatin inda ya yi kira ga jamaá su bujire ma yunkurin juyin mulkin.

Cikin yan watanni daga wannan lokaci Yeltsin ya kawo karshen tarayyar Soviet. A karshen waádin mulkin sa a shekarar 1999, farin jinin Yeltsin ta dakushe musamman saboda manufofin sa na tattalin arziki wanda ya jefa kasar Rasha cikin tsaka mai wuya. Kafin dai Boriya Yeltsin ya yi murabus daga karagar mulki yana daga cikin wadanda suka assasa dora shugaba mai ci a yanzu Vladimir Putin a kan mulkin Rasha.