1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Takaitaccen tarihin Donald Trump

November 9, 2016

An haifi Donald Trump a ranar 14 ga watan Yunin shekara ta 1946 a birnin New-York na Amirka.

https://p.dw.com/p/2SQJA
US-Präsidentschaftswahl 2016 - Sieg Donald Trump
Hoto: Reuters/M. Segar

Shi dai Donald Trump an haifeshi ne a ranar 14 ga watan Yunin 1946 a birnin New-York, ya na da shekaru 70 kenan a duniya. Tun a shekarun 1980 Donald Trump ya fara siyasa, amma kuma sai a zaben 2016 ne ya yi nasara zama dan takara shugabancin Amirka. Dukkanin manufofin da ya sa a gaba na jawo kace-nace musamman ma alkawarin gina katanga a kan iyakar kasarsa da Mexico idan ya lashe zabe. Ya samu jari ne da ya sarrafa daga mahaifinsa, lamarin da ya ba shi damar zamowa hamshakin attajiri, lamarin da Gwenda Blair ta yi tsokaci a kai:

 

"Ya yi imanin cewa kudi ne abu mafi daraja a duniya, saboda haka ne yake daukar neman kudi da muhimmanci. Trump da danginsu sun raja'a kan salon tunanin wani marubuci, wanda ya nunar da cewar yin aiki tukuru don cimma biyan bukata na da muhmmanci, idan ka tashi ko, to Allah zai taimakeka."

 

Marubutan tarihin Donald Trump na kwatanta shi a matsayin mutum mai tsananin wayo da zafin neman kudi. Ga shi kuma da kwarjini da alfahari da arzikin da Allah ya hore masa. Sai dai ba shi da kwakkwarar akida musamman ma a fannin siyasa. Ko da Gwenda Blair da ta rubuta litattafai biyu a kan Trump da iyalansa, sai da ta ce ya fi son kansa fiye da kowa.

USA Präsidentschaftswahl Donald Trump
Hoto: Reuters/C. Allegri

 

"Shi dan kasuwa ne da ya iya tallata kansa saboda ya yi imani da abin da yake yi. A wasu lokuta idan aka tinkare shi, aka gaya masa cewar ba a samu biyan bukata a wani abin da ya assasa ba, abin na bakanta masa rai. ya na nuna damuwarsa a fili."

Shima Tim O'Brien ya yi matukar nakaltar Donald Trump, saboda yana sahun gaba na wadanda suka bayyana a cikin littafin da ya rubuta cewar arzikin dan takarar Republican bai kai yawan wanda ya bayyana ba tun farko.

 

"Shi dai tamkar wani karamin yaro mai shekara bakwai mai suffar manya. Yana iya tsayawa ya yi aiki tukuru. Amma dai mutum ne da ba shi da ladabi a fanni mu'amala da mutane, sannan ba shi da tawali'in a fannin kudi ko da a bainar jama'a ne."

 

So uku ne Donald Trump ya sanar da cewar zai yi zawarcin kujerar shugabancin Amirka kafin daga bisani ya lashe amansa kamar yadda ya saba. Sai dai O'Brien na ganin cewar dan kararar Republican ya shiga harkokin siyasa sannu a hankali bayan da harkokinsa na kudi suka fara jan baya, inda ya tashi daga wanda ya mallaki dimbin gidaje zuwa mai hada shirye-shirye a talabijin.

USA Donald Trump Wahlkampf North Carolina
Hoto: Reuters/C. Keane

 

"Takarar Donald Trump na da nasaba da rikicin kudi da aka fuskanta a shekara ta 2008, saboda ya sa mutane da dama rasa aikinsu, sannan makomar masana'antun Amirka ta zama kila-wa-kala. Sun rasa damar da suke da ita ta biyan kudin makarantun 'ya'yansu da bashin da ake binsu. Wannan ya sa mafarkin samun makoma ta gari da ake da ita a Amirka ta fara fuskantar barazana."

 

Sai dai kuma Donald Trump ya yi nasarar kafa tarihi, inda ya kasance dan takarar shugabancin Amirka da bai bukaci taimakon kudi ba, sannan kuma bai kashe kudi na a zo a gani a yakin neman zaben da ya gudanar ba.