1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Takaita 'yancin 'yan jarida a kasashen Larabawa

Zainab MohammedFebruary 15, 2008

Dokar ragewa 'yan jarida 'yanci a yankin Larabawa

https://p.dw.com/p/D8DZ

Matakin da Ministocin yaɗa labarun ƙungiyar ƙasashen Larabawa suka cimma na amincewa da sabuwar dokar da zata bawa gwamnatoci ikon kulawa da ayyukan ƙafofin yaɗa labarai na Satelite,na mai zama wani mataki na take 'yancin 'yan jarida.
Wani shirin mahawara na mako-mako da wani dan jarida Wael Ibrashi ke gatarwa ta wani gidan talabijin mai zaman kansa a Masar,da ake kira Dream,Shri ne dake taɓo batutuwa na zahiri dangane da ainihin ababan dake gudana na yau da kullum wanda kuma jama'a ke jin daɗin kallon sa. A shekaru biyu da suka gabata dai akwai matsalar nan ta jiragen ruwa a Tekun Bahar Maliya,yanzu kuwa akwai yawan yajin aiki na maaikatan kamfanoni dake saka,ko kuma matsalar karancin ruwan sha a wasu yankunan dake makwabtaka da birnin Alkahira. Wannan doka da ministocin yaɗa labaran na ƙasashe Larabawan suka cimma dai,zai haifar da tsaiko adangane da yadda wannan shiri zai rika gudana da ma wasu siryr shirye dake kalubalantar yanayin tafiyar da ayyukan gwamnarti bisa ga irin matsalolin da jama'a ke fuskanta na rayuwa. Ministan yaɗa labarun ƙasar ta Masar Anas Fiqq yana mai raayin cewar." Ministocin harkokin yaɗa labaru na kasashen larabawa na yin shiru dangane da ayyukan wadannan kafofin yaɗa labarai na Satelite ne saboda,mafiyawa daga cikin su basu da wani aikin yi.Sukan koyi aikin ne ,kuma su dukufa cikin sa domin cimma nasu manufofi na siyasa kokuma kasuwanci,ba tare da la'akari da irin illan da zasuyi wa duniyar Larabawan ba" Haɗin kan al'umma da fannin rayuwa,da haɗin kan kasa,da bin doka da oder bisa ga tsari,batutuwa ne da bazasu ɓata cigaban kowace kasa baidan har ana daraja musu ,sai dai dangane da bukatau na addini da al'adun ƙasashen larabawan,inji ɗan jarida Wael Ibrashi... "Ko kaɗan hakan bai dace ba ,ace da irin waɗannan dokoki kafafen yaɗa labaru zasu gudanar da ayyukan su.Ta yaya za a ce baza'a kalubalanci yadda harkokin siyasa suke tafiya a kasashjen larabawa ba?Wannan kai tsaye tauya hakkokin 'yan jarida ne kawai ake neman yi" Tun a ranar talatar data gabat nedai gwamnatocin kasashen larabawn suka cimma amincewa da kafa wannan doka ta ke sa idanu tare da takaitawa kafafen yaɗa labaran ayyun su,daura da takaita bayanai kan harkoki na siyasa. An cimma wannan matsayi tare da amincewa da sanya shi cikin dokokin kasashen ne a taron ministocin kula da harkokin yaɗa labaru na kasashen yankin daya gudana a birnin Alkhahiran Masar. Manazarta dai sun bayyana wannan da kasancewa wani mataki ne na ɗauke 'yancin tafiyar da ayyukan su cikin walwala da 'yan jaridan kasashen larabawan ke dasu. Ministan yaɗa labaran kasar masar Anas ElFeki yace wannan doka ta wajaba akan dukkannin kasashen larabawan,duk dacewa kasar Qatar bata komai ba,kasancewar gidan Talabijin Aljazira dake taka rawa wajen faɗin gaskiyan lamura na girke ne a cikin ta.