Takaddamar Turkiyya da kasashen Turai | Labarai | DW | 03.04.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Takaddamar Turkiyya da kasashen Turai

Gwamnatin Turkiyya ta ce Turkawa mazauna ketare su yi zaben raba gardama duk da kin amince mata da aka yi.

Shugaban kasar Turkiyya Rajab Tayyib Erdogan ya yi kira ga Turkawan da ke kasashen Turai da su bijirewa wadanda ya kira ''Jikokin 'yan Nazi'' su kada kuri'ar raba gardamar da za a yi cikin wannan watan.

Wannan kiran da ma kalaman da shugaban na Turkiyya ya yi amfani da su dai, na iya ta'zzara lamura tsakanin Turkiyya da kasashen na Turai ciki har da kasar Jamus da ya yi amfani da munanan kalamai a kanta a baya.

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel musamman ta yi gargadi ga shugaba Erdogan da ya daina amfani da kalaman danganta kasar Jamus da yakin shekarun da suka shude.

Shi dai shugaba Erdogan ya bukaci kasashen Turan ne da su kyale a yi zaben raba gardama wa Turkawan da ke kasashensu ne, don bashi damar sauya tsarin mulin kasar don ya sami karfin iko.