1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Takaddamar shirin nukiliyar kaar Iran

Mohammad Nasiru AwalAugust 1, 2005

Iran ta ce a yau litinin zata fara wani takaitaccen aikin sarrafa uranium.

https://p.dw.com/p/Bvag
Shugaban Iran mai jirar gado Ahmadinejad
Shugaban Iran mai jirar gado AhmadinejadHoto: AP

A ran 20 ga watan yuli wakilan KTT EU da na Iran suka gana a birnin London, inda suka amince cewa daga karshen watan na yuli zuwa farkon watannan na agusta za´a gabatarwa gwamnatin birnin Teheran wani tayi wanda zai jawo hankalin wannan janhuriya da ke bin tsarin Islama ta dakatar da shirin samar da sinadarin uranium.

Wannan tayi kuwa ya hada da ba ta taimako don amfani da fasahar nukiliya a hanyoyin lumana da karbar ta cikin kungiyar cinikayya ta duniya sai kuma kulla wata yarjejeniyar ciniki ta musamman tsakanin kungiyar EU da Iran.

Amma a ranar asabar da ta gabata kasashen Turan sun tuntubi Iran don ta kara musu wannan wa´adi ya zuwa 7 ga watan agusta, domin kamar yadda suka nunar a wannan lokaci sabon shugaban Iran, Mahmud Ahmedi-Nejad wanda za´a rantsad da shi a ranar 6 ga watan na agusta ya kama aiki. To amma hukumomi a birnin Teheran sun yi watsi da haka kamar yadda kakakin ma´aikatar harkokin waje Hamid-Reza Assefi ya nunar ya na mai cewa:

„Tun a birnin London muka fadawa Turawan cewa a karshen watan yuli wa´adin zai kare. Saboda haka mun sa rai zasu gabatar da shawarwarin, amma sai kwatsam mu ka ji cewa an yiwa daftarin shawarwarin canje-canje masu yawa.“

To sai dai ba´a sani ba ko lalle kasashen Turan sun yi wadannan canje-canje. Hukumomin Teheran na zargin cewa sai da kasashen Turan su ka tuntubi gwamnatin Washington, wadda tun da farko niyar ta ita ce a mika batun nukiliyar Iran din ga kwamitin sulhu na MDD.

Yanzu dai hukumomin a Teheran sun kudurin aniyar fara wani takaitaccen aikin sarrafa karafan uranium a yau litinin idan kasashen Turan ba su gabatar da sabbin shawarwarin ba, inji Assefi.

„Zamu fara aikin nukiliyar a tashar Isfahan. To amma duk da haka za mu takaita aikin kamar yadda muka alkawarta. Saboda haka ne ma za mu fara da karamar tashar nukiliya ta Isfahan, amma ba a Natanz ba, inda ake iya sarrafa uranium. A shirye mu ke mu tattauna dangane da tashar ta Natanz.“

A halin da ake ciki wakilan hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa sun isa birnin Teheran kuma suna iya tashi zuwa Isfahan a ko wane lokaci, to amma da alama ana samun rarrabuwar kawuna a cikin gwamnatin Iran dangane da lokacin da za´a bude tashar ta Isfahan, wato ko da yammacin yau litinin ko kuma da sanyin safiyar gobe talata.

Wata majiya ta rawaito mai ba gwamnatin Iran shawara a harkokin tsaro Agha Mohammadi na cewa ana iya jira har sai ranar 7 ga watan nan na agusta idan suka samu tabbaci daga kasashen Turai. Har in haka ta samu, to ke nan za ta yi daidai da sabon yanayin siyasa da za´a shiga a Teheran. Domin a ranar laraba shugaban addinin kasar Ayatollah Khameni zai gabatar da sabon shugaba Ahmedi Nejad sannan a rantsad da shi a gaban majalisar dokoki a ranar asabar wato 6 ga wata.