Takaddamar shirin nukiliyar Iran | Labarai | DW | 20.11.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Takaddamar shirin nukiliyar Iran

Iran ta ce ba zata ba da izinin kai ziyarar ba zata a tashoshin ta na nukiliya ba, idan aka mika takaddamar da ake yi da ita game da shirinta na nukiliya ga kwamtin sulhun MDD. Hukumomi suka ce idan aka yi haka to zata fara aikin sarrafa sinadaran Uranium kamar yadda majalisar dokoki a birnin Teheran ta amince. A ranar alhamis hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa zata yi shawarwari a birnin Vienna a game da shirin nukiliyar Iran din. Hukumar ka iya yin karar gwamnatin Teheran a gaban kwamitin sulhu wanda shi kuma zai iya kakaba mata takunkumi.