Takaddamar Rasha da Belarus
June 23, 2010Talla
Ƙasar Rasha ta rage iskar gas da take turawa ƙasar Belarus da kimanin kashi 60 cikin ɗari, wannan ya biyo bashin da Rasha ke bin ƙasar ta Belarus na fiyeda euro miliyan 160. Shugaban kamfanin Gazprom mallakar gwamnatin Rasha, shine ya bada umarnin taƙaita gas da ake turawan, bayan da shugaban ƙasar Belarus ya sanar da rufe bututun iskar Gas da Rahsa ke turawa ƙasashen Turai, wanda ya ratsa cikin ƙasar ta Belarus. Dama dai tun a jiyane Rasha ta rage iskar gas da take turawa Belarus da kashi 15 cikin ɗari, abinda kuma ya tunzura Belarusawan. Ita dai ƙasar Rasha ta bayyana cewa, wannan taƙaddamar ba za ta katse tura gas da take yiwa kwastomominta dake Turai ba.
Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Umaru Aliyu