Takaddamar Amirka da kasashen Larabawa | Siyasa | DW | 27.01.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Takaddamar Amirka da kasashen Larabawa

Al'umomin kasashen Larabawa da shugabanninsu, na ci gaba da mayar da martani kan sababbin matakan da Donald Trump ya dauka na hana takardar izinin shiga kasarsa ga al'ummar wasu kasashe.

Kasashen da wannan doka ta shafa a yanzu sun hada da Siriya da Iraki da Yemen da Libiya da Sudan da kuma Somaliya. Ilyas Atiyah wani kirista dan kasar Iraki da ke zaune a sansanin 'yan gudun hijra a yankin Arbeel na Kurdawa ya ce matakin yayi matukar kashe ma su gwiwa. Shima Haidar Salmani wani dan gudun hijira na Siriya da ke kasar Turkiya, wanda ke cike da burin zuwa Amirka ya ce matakin da Trump din yake son dauka a kasarsa domin hana kwararar 'yan gudun hijirar zuwa kasar ya saba wa tsarin demokaradiyyar da Amirkan ta jima tana rajin yada wa a duniya. Husam Adnan wani magidanci dan kasar Yemen da 'yarsa ta gabatar da takardar neman zuwa Amirka domin karin karatu, ya ce, matakin na Mr Trump zai zame wa Larabawa izna su san cewa, ba mai sosa maka bayanka fiye da faratunka:

 

Jemen Flüchtlingsfamilie aus Syrien (DW/M. al-Haidari)

Wani dan kasar Yemen da iyallansa

 "A gaskiya dama an ce a rashin uwa akan yi uwar daki. Idan da shugabanninmu sun yi mana abun da ya wajaba, da ba za a yi mana irin wannan wulakancin ba.Yanzu dabara ta rage ga mai shiga rijiya, ko dai shugabanninmu su gyaramu, ko kasashen duniya su yi ta wulakanta mu."

 Shi kuwa Gamal Khashfajy, wani marubuci dan kasar Saudiya, a ganinsa duk da cewa kasarsa bata cikin kasashen da dokar ta shafa ya wajaba Larabawa su kalli matakin na Trump da kyakkyawar manufa:

 "A ganina, Trump, munyi masa mummunar fahimta. Domin hakika baya barazana ga muradinmu. Matakan da yake dauka na kare kasarsa, muma irunsu muke dauka a kasashenmu. Shi mutum ne da bashi da kumbiya- kumbiya.Yakan kira komi da sunansa baki ne ko fari ne.

 

Sauti da bidiyo akan labarin