Takaddamar Afirka ta Kudu da EU | NRS-Import | DW | 01.02.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

NRS-Import

Takaddamar Afirka ta Kudu da EU

Masu kiwon kaji a Afirka ta Kudu sun koka da cewa suna daf da durkushewa sakamakon kaji masu arha da kungiyar Tarayyar Turai EU ke shigar wa cikin kasar.

Shugaban kasar Afirka ta Kudu Jacob Zuma

Shugaban kasar Afirka ta Kudu Jacob Zuma

EU din dai na shigar da kajin Afirka ta Kudu ne a wani bangare na kasuwanci mara shinge a tsakaninsu. Kungiyar ta EU dai ta musanta hakan, tana mai zargin masu kiwon kajin ta fakewa da guzuma kawai, inda ta ce kajin da take shiga dasu Afirka ta Kudun basu taka kara sun karya ba, kana ba zasu iya yin katabus ba wajen gurgunta masana'antar kiwon kajin. Kimanin masu kiwon kaji 500 a Afirka ta Kudun ne suka yi wani tattaki zuwa shalkwatar kungiyar ta EU da ke birnin Pretoria da nufin nuna bacin ransu, inda suka koka da cewa tuni mutane 4,000 zuwa 5,000 suka rasa abin yi yayin da wasu 110,000 ke fuskantar brazanar raasa sana'arsu.