1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Takaddama tsakanin Obasanjo da Jonathan

January 9, 2013

Tsohon shugaban Najeriya Cif Olusegun Obasanjo ya soki lamirin gwamnati game da rashin daukar kyawawan matakan shawo kan matsalar tsaro da kasar ke fuskanta.

https://p.dw.com/p/17GoL
Hoto: Katrin Gänsler

Kalaman da tsohon shugaban Najeriya Cif Olusegun Obasanjo ya yi a game da gazawar gwanatin Najeriya wajen amfani da hanyar sulhu da hanyar karfi a kokarin shawo kan matsalar masu kai hare-hare na ta'addanci a kasar ya sanya duba lamarin da illar da ke tattare da matakin da gwamnatin ke dauka a kan wannan lamari.

Fitowa kara a fili da toshon shugaban Najeriya Cif Olusegun Obasanjo ya yi na cewar gwamnatin Najeriyar fa ba ta kama hanyar da ta dace ba wajen shawo kan matsalar ta 'yan kungiyar ta Ahlu Sunnah Waljihad na zaman matakin baya-baya nan da wani jigo a kasar ya fuskancin gwamnatin domin amaye abinda ke a zuciyarsa.

Cif Olusegun Oabsanjo da a 'yan kwanakin nan kan bigi kirji ya bayyana ra'ayinsa a game da matsalolin da ke kalubalantar kasar, ya ce akwai bukatar gwamnatin daukan salon a ciza a hura a game da wanan matsala ta rsahin tsaro da mutane da dama kan fake da cewa matsala c eta talauci. Malam Hussani Mongunu masani ne a harkokin tsaron Najeriyar ya bayyana yadda yake kallon wannan lamari.

Nigeria Polizei Polizisten auf Patrouille in Bauchi
Hoto: Getty Images/AFP

Gazawar hukumomi wajen magance matsalar tsaro

"Babu wani wanda ya mallaki hankalinsa a Najeriya da zai bayyana maka cewa dubaru da sidabaru da ake amfani da su a game da batun sha'anin tsaro ko kuma batun Boko Haram a Najeriya zai iya amfani da wani abu. Saboda haka maganar da shi ya fada shi tsohon shugaban kasa ne, tsohon janar na soja ne wanda ya yi yaki, maganar da ya fada haka yake, da ma irin maganganun da muka sha fada kenan a kan wannan lamarin ba su kai ga haihuwar da mai ido ba. Saboda haka dole ne a zauna a tattauna a shawo kan wannan rigimar. Amma in dai ana so a shawo kanta to ba'a ma dauko hanya ba."

To sai dai shugaban Najeriyar Goodluck Jonathan ya dade yana nanata cewar gwamnati a shirye take da ta tattauna da kungiyar domin samun mafita, sai dai ba za su yi hakan ba har sai kungiyar ta bayyana kanta a fili, abinda kwararru a fannin tsaro ke sukar cewa tayin da 'ya'yan kungiyar suka yi ya isa a ce gwamnatin ta yi amfani da shi. Mr. Labaran Maku shi ne ministan kula da yada labaru na Najeriya ya ce akwai bukatar fahimtar lamarin yadda yake.

Bombenanschlag Nigeria
Hoto: picture-alliance/dpa

"Gwamnati muna nan muna aikinmu a kan batun tsaro in kaje nan yanzu za ka ga akwai sojoji akwai 'yan sanda suna aiki ba dare ba rana, kuma ana samun nasara. Sai dai kawai ba za mu kammala komai duka ba. Abinda muke kira shi ne mutane su taimaka wa gwamnati, amma mun san kowa a nan mun san masu laifi, amma in baka daraja mutum ba ya za ka daraja Ubangiji domin shi ne mafita."

Hanya sulhu ita ce mafita

Batun amfani da hanyar sulhu domin samun mafita daga batun na kungiyar Ahlu Sunnah Li Da'awati Wal jihad dai ya kasance wanda ke fuskantar adawa mai karfi musamman daga kungiyar Kristocin Najeriya.

Ganin irin yadda ake zargin raba gari a tsakanin gwamnatin Najeriyar da tsohon shugaban kasar Olusegun Obasanjo da a lokutan baya akewa kalon mai uwa da makarbiya a gwamnatin na zaman abinda za'a sa ido a ga tasirin tunkarar gwamnatin da ya yi da wannan magana mai karfi a yanzu.

A yanzu dai babu wani kalubale na zahiri da yafi tsayawa mahukuntan Najeriyar a wuya irin na batun kai hare hare a cikin kasar wanda ake ganin akwai bukatar gwamnati ta nuna da gaske ta ke a kan ikirarin da take na shawo kan matsalar.

Mawallafi: Uwais Abubakar Idris
Edita: Mohammad Nasiru Awal