1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

CDU da CSU a Jamus na cigaba da takaddama

Mohammad Nasiru Awal AH
June 15, 2018

Ana ci gaba da kai ruwa rana tsakanin jam'iyyun hadin gwiwa na CDU da CSU a Jamus dangane da batrun 'yan gudun hijira.

https://p.dw.com/p/2zckw
Angela Merkel da Wolfgang Schäuble
Angela Merkel da Wolfgang Schäuble Hoto: Reuters/F. Bensch

'Ya'yan jam'iyyar CDU ta shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel sun musanta wani rahoto da ke cewa an yi kira ga shugaban majalisar dokokin kasa Wolfgang Schäuble da ya shiga tsakani don yin sulhu tsakanin jam'iyyun kawance na CDU da CSU a kan batun 'yan gudun hijira.

'Yan siyasa daga jam'iyyar CDU sun ce ba a nemi Schäuble don ya taimaka a samu maslaha a takaddamar da ake yi tsakanin jam'iyyun biyu kuma kawayen juna wato CDU da CSU kan manufar gwamnati da ta shafi yin kaura da hijira a kasar ba.

Bambancin ra'ayi da ya kamari tsakanin Merkel da ministan cikin gida kuma shugaban jam'iyyar CSU Horst Seehofer kan batun na 'yan gudun hijira na barazanar ruguza gwamnatin 'yan ra'ayin mazan jiya da yanzu ke jan raganmar gwamnatin hadin gwiwa da jam'iyyar SPD a Jamus.

A wannan Jumma'a jaridar Rheinische Post ta ruwaito cewa jam'iyyar CDU na ganin Schäuble a matsayin mutumin da sassan biyu ke mutuntawa dangane da adawarsa da manufofin Jamus kan 'yan gudun hijira a da da kuma yadda yake biyayya da Merkel sau da kafa.