1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Takaddama na ci gaba a game da shirin nukiliyar Iran

August 11, 2005

Ana ci gaba da daukar matakai na diplomasiyya domin shawo kan rikicin nukiliyar Iran, sai dai babu shaidar dake tabbatar da cewar kasar na da niyyar sarrafa makaman kare dangi

https://p.dw.com/p/BvaV

Ita dai hukumar makamashin nukiliya ta kasa da kasa dake da shelkwatarta a birnin Vienna ba ta da laifi a take-takenta dangane da kasar Iran. Kasashen da suka nuna gazawa a wannan manufa sun hada ne da Faransa da Birtaniya da kuma Jamus, wadanda suka kasa gabatar da wata takamaimmiyar shaida a game da ikirarin da kasashen Amurka da Isra’ila ke yi na cewar hakkun ne kasar Iran na fafutukar sarrafa makaman nukiliya. Wajibi ne a nemo shaidar dake tabbatar da wannan ikirari, amma ba dogara akan tsinci-fadin da wasu ‚yan adawar kasar Iran dake zaman hijira a ketare suke yayatawa ba. A dai halin da muke ciki yanzun babu irin wannan shaida kuma babu wata alamar dake nuna cewar za a same ta. Ita dai hukumar makamashin nukiliya ta kasa da kasa ba zata iya dogara akan jita-jita domin tsayar da kuduri ba. Sifeticin hukumar na bukatar wata tabbatacciyar shaida da zata kawar da dukkan tababa akan manufa. A zamanin baya kasar Amurka ta nuna wa hukumar fin karfi dangane da kasar Irak, amma a wannan karon ga alamu hukumar ke da galaba. Wannan ci gaba ne dake da muhimmancin gaske domin kauce wa wani yanayi, inda wasu kasashe, a sakamakon matsayinsu na soja zasu rika amfani da jita-jita domin barazanar nuna karfin hatsi ba gaira-ba-dalili. Ko shakka babu akwai abubuwa da dama dake yin nuni da cewar kasar ta Iran ba kawai zata yi amfani da tashar nukiliyar ne domin samar da wutar lantarki ba, amma a daya bangaren kasar ta cika dukkan sharuddan da aka gindaya na hana yaduwar fasahar sarrafa makaman nukiliya. Bugu da kari kuma dukkan matakan da ta dauka da kuma wadanda take dauka yanzu haka a Isfahan ba su saba da kudurorin yarjejeniyar hana yaduwar fasahar ta sarrafa makaman nukiliya ba. Ta la’akari da haka zai zama tamkar cin mutunci ne ga kasar ta Iran idan wasu kasashe na Turai suka tinkareta domin neman wasu bayanan da ba wajibi ba ne ta gabatar da su a karkashin yarjejeniyar, wacce ba dukkan kasashen dake da fasahar sarrafa makaman nukiliya ne ke da hannu a cikinta ba. Ba da kai bori ya hau ga bukatun kasashen Turai da Amurka zai zama tamkar mayar da hannun agogo baya ne zuwa ga wani zamanin da ya shude, lokacin da kasashen na Turai da Amurka ke zayyana wa Iran alkiblar da zata fuskanta game da manufofinta. Wannan maganar tana kada zukatan al’umar Iran kuma lokaci yayi da kasashen Turai da Amurka zasu ankara da haka. Wajibi ne su canza salon kamun ludayinsu, su dawo daga salonsu na mulkin mallaka a ma’amalla da kasashe kamar Iran. Tilas ne a kakaba wa Iran takunkumi idan har tayi fatali da yarjeniyoyi na kasa da kasa, amma kawo yanzu babu wata shaidar dake nuna haka.