Takaddama kan sabon zaben Kenya | Labarai | DW | 05.09.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Takaddama kan sabon zaben Kenya

'Yan adawa na Kenya sun yi fatali da zabe ranar 17 ga watan Oktoba da hukumar zaben kasar ta tsayar domin sake zaben da kotun koli ta soke.

Jagoran 'yan adawa na kasar Kenya Raila Odinga ya yi fatali da sabuwar ranar da hukumar zabe da tsayar domin sake gudanar da zaben shugaban kasa da kotun koli ta soke. 'Yan adawa suna neman ganin aiwatar da zaben tsamanin ranakun 24 da 31 ga watan Oktoba, amma gwamnati tana ganin haka zai shafi lokacin rubuta jarabawa na dalilai. Ita hukumar zaben ta saka ranar 17 ga watan Oktoba domin yin sabon zabe.

Sannan Odinga ya nuna damuwa da yadda hukumar zaben ta hana sauran 'yan takara shiga zabe. Kana 'yan adawa suna neman ganin hukuntan jami'an hukumar zabe wadanda suka gaza, abin da ya janyo kutun koli ta soke zabe. Ana sa ran yin gumurzu tsakanin Shugaba Uhuru Kenyatta da jagoran 'yan adawa raila Odinga, yayin zaben na Kenya, idan komai ya tafi kamar yadda aka tsara.