1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Takaddama akan sallamar wasu kusoshin jam'iyar MNSD Nasara a Nijar

February 14, 2014

Kusoshinta tara ne jam'iyar MNSD Nasara mai adawa a Nijar ta sallama bisa yin karan tsaye ga dokokinta.

https://p.dw.com/p/1B9Yv
Alhaji Saini Oumarou Oppositionspartei MNSD Nasara im Niger
Hoto: DW/M. Kanta

A jamhuriyar Nijar babbar jamiyyar adawa ta kasar ta MNSD NASARA ta dauki matakin tsige wasu daga cikin kusoshinta guda tara wadanda ta ke zargi da aikata laifin kin mutunta dokokin jam'iyar bayan da suka amince suka karbi mukamai a cikin gwamnati mai ci yanzu, ba tare da lamuncewar uwar jam'iyar tasu ba. Sai dai mutanen da jam'iyar ta ce ta dauki matakin tsige su din sun ce ba su tsigu ba domin matakin ya sabawa dokokin jam'iyar tasu.

Matakin korar da jam'iyar ta MNSD Nasara ta dauka biyo bayan wani zaman taron da komitin kolin na kasa ya gudanar a yammacin wannan Alhamis (13.02. 14) ya shafi wasu kusoshin jam'iyar guda tara da suka hada da Malam Albade Abuba, magatakardan jam'iyar na kasa kana shugaban jam'iyar na jahar Tahoua da Malama Alma Ummaru shugabar jam'iyar na reshen jihar Damagaram da kuma Malam Amadu Salifu, shugaban

jam'iyar na reshen birnin Yamai. Sai kuma Malam Wasalke Boukari da Malam Ada Shefu, dukkanninsu na jihar Tillabery.

Shugaban Nijar, Mahamadou Issoufou
Shugaban Nijar, Mahamadou IssoufouHoto: picture alliance/dpa

Sauran kuwa sun hada ne da Malam Hasan Yeli na jahar Tahoua da Malam Mahamadu Zada na jihar Dosso da Malam Siraji Isaka na jihar Damagaram. Sai kuma Malam Isufu Umaru na jihar Maradi, dukkaninsu jam'iyar tasu na zarginsu da shiga gwamnati ba tare da lamincewar uwar jam'iya ba, wacce ke jagorancin jam'iyar adawar kasa a yanzu haka.

Dalilin sallamar wasu kusoshin MNSD Nasara

Malam Isufu Tambura, sakataren yada labarai na jam'iyar ta MNSD Nasara, ya yi karin bayani dangane da wanann mataki da jam'iyar tasu ta dauka.

Daga cikin kusoshin jam'iyar guda tara da wannan mataki na tsigewa ya shafa kuwa akwai hudu masu rike da mukamin minista a cikin gwamnati, a yayin da wasu ke rike da mukaman manyan daraktocin kamfanonin gwamnatin kasar ta Nijar, kuma tuni suka bayyana rashin amincewarsu da wannan mataki da aka dauka a kansu, kamar dai yanda Malam Albade Abuba wanda ake yiwa kallon jagoran wadanda jam'iyar ke kira 'yan tawaye ya shaida a cikin martanin da ya mayar.

Seini Oumarou Vorsitzender der Partei MNSD im Niger Afrika
Seini Oumarou, jagoran MNSD NasaraHoto: MNSD

Kalubalantar matakin sallama daga jam'iya

Yanzu haka dai wadannan mutane da jam'iyar ke bayyanawa a matsayin 'yan tawaye, sun sha alwashin kai dambe a tarna inda suka kira wani taro a wannan Asabar (15. 02. 14) a garin Tillabery, mahaifar shugaban jam'iyar ta MNSD Nasara Alhaji Seini Omar, domin a cewarsu kalubalantarsa har a gida.

Matsawar da jam'iyar ta MNSD Nasara ta yi daga Yunkurin da ta yi a baya na shiga gwamnatin hadin kan 'yan kasa da shugaban kasa Alhaji Mahammadu Isufu ya yi masu tayi dai, shi ne dai ya haddasa rabuwar wutsiyar kaza tsakanin 'ya'yan jam'iyar ta MNSD Nasara inda wasu ke a cikin gwamnati, wasunsu kuma na a bangaren adawa.

Mawallafi : Gazali Abdou Tasawa
Edita : Saleh Umar Saleh