Takaddama a majalisar dokokin Nijar | Siyasa | DW | 12.11.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Takaddama a majalisar dokokin Nijar

Ba zato ba tsammani 'yan majalisar suka ajiye wata takarda dauke da jerin bukatunsu na gurfanar da shugaban kasa a gaban kuliya.

A yayin da majalisar dokokin kasar ta jefa kuri'ar amincewa da sabon kasafin kudi na sabuwar shekara wata sabuwar takaddama ce ta barke a majalisar dokokin inda 'yan adawa suka gabatarwa majalisar takardar bukatar tsige shugaban kasar bisa zarginsa da cin amanar kasa, 'yan adawar dai sun jera irin zarge-zargen da suke tuhumar shugaban kasa da aikatawa matakin da ya haifar da cece-kuce a majalisar. Sai dai bangaren masu mulki sun kalubalanci matakin na yan adawa suna masu cewar sun yan adawar sun shigar da takardar ne ba akan ka'ida ba.


'Yan majalisun dokokin na adawa sun ce ba zasu taba yarda ba suna zura ido hukumomin kolin kasar na ci gaba da yiwa dokokin kolin kasa hawan kawara da yin kaca-kaca da kundin tsarin mulkin kasar alhali kuwa sun karbi rantsuwa wani bi harma da Al'kur'ani da za su yi ingantaciyar biyayya ga dokokin tsarin mulki, takardar dai da 'yan adawar suka shigar kumshe take da zarge zarge har guda uku kuma na tuntubi kakakin kawancen yan adawar a majalisa Hon Tidjani Abdoul kadri don Karin bayani


Sitzung der Nationalversammlung in Niamey Niger

"Duk diyoyi da lahohin kudaden ma'adinan karkashin kasa na yarjejeniyar da ake yi a zuba su a cikin baitilmali na kasa a matsayinsa na shugaban kasa da yayi rantsuwa kan cewar zai kiyaye a kan kudaden an zubasu sai yake bari suna wucewa ba'a san inda suke shiga ba, na biyu an kama wasu makuddan kudade a filin jirgi kusan biliyan tara aka kama da gagawa aka ce a mayarwa wadanda ke da wadannan kudaden kudinsu kuma shugaban kasa ya sani yayi kunnen uwar shegiya kansu yayi kamar bai sani ba to wadannan abubuwan manya manyan abubuwa ne da suka sabawa kundin tsarin mulki da dokokinmu saboda wadannan dalilan ne muk shigar da wannan takarda muk ce ya kamata muna kira ga 'yan majalisa da su bamu goyon baya da su kama muna mu dakatar da wannnan mulkin na Hitler.


Martanin jam'iyya mai mulki

Tuni yan majalisun dokokin kawancen jam'iyyun dake mulki sukayi fatali da sabon yunkurin na yan adawa suna mai cewar yunkurin ya sabawa kundin tsarin mulki da ma duk wasu ka'idodin jamhuriya da ke baiwa da majalisa damar shigar da wata bukata a gaban shari'a. Hon Zakari Oumarou shugaban rukunin 'yan majalisun jam'iyyar PNDS tarayya ne mai mulki.


"Sun dauko takarda sun ba da kuma sun ce suna da 'yan majlisa 33 da suka saka hannu kuma kundin tsarin mulki bai yi bayani a kan wannan ba. To tunda babu bayani mu zamu yi watsi da shi ke nan. A cikin duhu suka yi hakan dole zasu tunkari wannan kotun da suka ce basu yarda da ita ba a da haramtacciya ce domin ta basu bayani kuma duniya kowa ya gano da cewar kotun nan da basu yarda da ita bane basu son tunkarar zabe ne".

To amma haka aka yi kuma lokacin da kuka shigar da bukatar tsige tsohon kakakin majalisa Hama Amadou bak a ganink amar hanyoyi daya ne su ma suka bi?

"Ehh ba daya bane amma in ya zama daya ne mu fa ba tsoron mahawarar muke ba muna son a zo a zauna abin nan da suke fadi a cikin kafafen yada labarai muzo muyi mahawa das u a bayya ne duniya ta sheda cewar ba gaskiya bane."


A 'yar doka mai lamba 142 zuwa 144 ta kundin tsarin mulkin Nijar sun bayyana yanda ake bi domin gurfanar da shugaban kasa a gaban kuliya idan har aka zargesa da cin amanar kasa, sai dai wasu masharhanta na cewar tsarin tafiyar da ayyukan majalisar bai fayyace dalla-dalla ba ta yanda 'yan majalisa zasu bi domin shigar da bukata.

Sauti da bidiyo akan labarin