Takaddama a kan shirin nukiliyar Iran | Labarai | DW | 25.11.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Takaddama a kan shirin nukiliyar Iran

Kungiyar Tarayyar Turai ta yi suka da kakkausar lafazi game da take-taken kasar Iran akan shirin ta na nukiliya da ake takaddama a kai. Kungiyar ta EU ta yi barazanar mika wannan batu ga kwamitin sulhun MDD. Bayan wani taro da majalisar gwamnonin hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa ta yi a birnin Vienna an jiyo dan diplomasiyar kasar Birtaniya Peter Jenkins na magana a madadin kungiyar EU cewa take-taken Iran ya sa ana shakku game da gaskiyar cewar shirin ta na nukiliya na lumana ne amma ba na kera makamai ba. Mista Jenkins ya ce kofofin yin shawarwari ta diplosiya ba zasu kasance a bude har abada ba. Jenkins ya ce watakila a cikin watan desamba kasashen Birtaniya, Jamus da Faransa zasu sake yin shawarwari da Iran, don sake gabatar ma ta da shawarar da Rasha ta bayar game da sarrafawa Iran din sinadarin Uranium.