1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Takaddama a kan shirin nukiliyar Iran

Shugaban hukumar kula da nukiliya a Iran Gholamreza Aghazadeh ya ce kasar sa zata samar da sinadarin uranium da kuma makamashin nukiliya duk da kokarin da kasashen duniya karkashin jagorancin Amirka ke yi na dakile wannan shiri. Aghazadeh ya fadawa wani taron manema labarai cewa ko shakka babu za´a cimma burin samar da makamashin nukiliya a Iran. Aghazadeh wanda har wala yau yana daya daga cikin mataimakan shugaban kasar Iran bai fadi lokacin da za´a fara wannan aiki ba. A game da tayin da kasasshen Turai su yi na ta bari Rasha ta sarrafa mata sinadarin Uranium mataimakin shugaban ya ce ba za´a yarda da alkawuran kasashen Turai ba.