Takaddama a game da dokar kodago a Faransa | Labarai | DW | 20.03.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Takaddama a game da dokar kodago a Faransa

P/M Faransa Dominique de Villepin ya ce gwamnatin sa ba za ta sauya matsayi ba a game da sabuwar dokar kwadago duk da barazanar da yan ƙungiyoyin kwadago suka yi na gudanar da yajin aikin gama gari idan gwamnati ba ta janye dokar ba. A wata ganawa da ya yi da manema labarai de Villepin yace wajibi ne a bar doka ta yi aikin ta. Dokar wadda aka tsara da nufin rage zaman kashe wando a tsakanin matasa, ta kuma baiwa hukumomi damar sallamar maáikata a farkon shekaru biyu na sanin makamar aiki, ba tare da sanar da maáikatan hujjar sallamar ba. Dubban jamaá sun gudanar da zanga zanga a manyan titunan birnin Paris domin baiyana adawar su da wannan sabuwar doka. An yi ta dauki ba daɗi tsakanin yan sanda da matasa masu zanga zanga.