Taimakon Raya Kasashe Masu Tasowa | Siyasa | DW | 12.04.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Taimakon Raya Kasashe Masu Tasowa

Kungiyar Tarayyar Turai na so ta canza salonta na ba da taimakon raya kasa

Babban abin da Ƙungiyar Tarayyar Turai ke bukatar gani shi ne dora manufofinta na taimakon raya ƙasashe masu tasowa akan wata sibga mai tasiri da rafusa da kuma rashin dogon turanci. Wannan shi ne babban burin da ministocin taimakon raya ƙasashe masu tasowa na ƙungiyar suka sa gaba. An saurara daga kantoman ƙungiyar ta tarayyar Turai akan manufofin raya ƙasashe masu tasowa Louis Michel yana mai bayani a game da muhimmancin wannan matsala tare da ba da misali da ƙasar Tanzaniya, inda yake cewar:

“Ƙasa kamar Tanzaniya dake da shugabanci na gari kuma ba ta da wani ƙaƙƙan matsayi ta kan karɓi baƙoncin tawagogin wakilai sama da 250 daga kafofi daban-daban masu ba da lamuni a duk shekara. Wato dai a taƙaice hakan na ma’ana ne cewar ƙasar kan karɓi baƙonci wata tawaga bayan kowaɗanne sa’o’i 24 dake hallara ƙasar dauke da sharuɗɗa da ƙa’idoji daban-daban. Ta’akari da haka ba zai zama abin mamaki ba idan an yi batu a game da yadda al’amura kan kai wa ƙasashen Afurka dake samun taimakon iya wuya.”

To sai dai kuma har yau ƙasashe kamarsu Sweden da Denmark dake arewacin Turai na adawa da manufar haɗin kan matakan taimakon, lamarin da ke ci wa Louis Michel tuwo a ƙwarya. Kantoman na Ƙungiyar Tarayyar Turai akan manufofin taimakon raya ƙasashe masu tasowa ya sha nanata cewar ba ƙokari ne shelkwatar ƙungiyar a Brussels take yi domin neman ƙarin iko ba, abu ne da ya shafi ainifin shi kansa taimakon da ake bayarwa. Kantoman dai na samun cikakken goyan baya daga ministar taimakon raya ƙasashe masu tasowa ta Jamus Heidemarie Wieczorek-Zeul, wadda take alla-alla ta ga al’amura sun ɗauki wani sabon fasali mai ma’ana. Amma abin takaici a taron na Brussels a jiya talata ba a cimma daidaituwa akan manufar ta bai daya ba, ko da yake Wieczorek-Zeul tayi madalla da kyakkyawar niyyar da aka nuna a sanarwar bayan taro. Takamaimiyar daidaituwar da aka cimma dai ita ce game da ci gaba da tallafa wa matakan kiyaye zaman lafiya da Ƙungiyar Tarayyar Afurka ke ɗauka tare da tsabar kuɗi Euro miliyan 300 a cikin shekaru uku masu zuwa. Sai kuma maganar yafe basussuka da taimakon gaggawa ga kasashen dake fuskantar bala’i daga Indallahi irin shigen ambaliyar nan ta tsunami. A taron na bana daidai da wanda ministocin suka gudanar a shekarar da ta wuce an tsayar da shawarar mayar da hankali sosai da sosai ga ƙasashen Afurka da suka fi fama da raɗaɗin talauci. A wannan ɓangaren kamar yadda ministar taimakon raya ƙasashe masu tasowa ta Jamus ta nunar Ƙungiyar Tarayyar Turai zata yi bakin ƙoƙarinta wajen shawo kan sauran ƙasashen dake ba da taimako kamar Amurka da su dakatar da nuna son kai. Ministar ta ce bai kamata neman cin gajiyar albarkatun ƙasa ya zama shi ne a’ala wajen ba da taimako ba:

Ainifin abin dake akwai shi ne bai wa ƙasashen Afurka wata kyakkyawar kafa ta cin gajiyar albarkatun ƙasa da Allah Ya fuwace musu domin yaƙar talauci da kuma raya makomarsu. A saboda haka ya zama wajibi a samu haɗin kan manufofin taimakon tsakanin ƙasashen Ƙungiyar Tarayyar Turai a ɓangare guda da kuma sauran ƙasashen dake ba da taimakon a ɗaya ɓangaren ta yadda kwalliya zata mayar da kuɗin sabulu dangane da bu—katar da aka sa gaba.